Sabuban Soyayyao- Karamci
76. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mai karimci abin kauna ne gun Allah abin baiwa lada, kuma abin so ne mai kwarjini a wajen mutane[35]. p- Kawaici
77. Imam Ridha (A.S): daga cikin alamomin ilimi shi ne; hakuri, da ilimi, da kawaici. Hakika kawaici kofa ce daga kofofin hikima. Hakika kawaici yana kawo soyayya. Shi ne jagora ga dukkan alheri[36]. k- Baiwa
78. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: kyauta tana kawo soyayya, kuma tana kawata kyawawan halaye[37]. 79. Daga gareshi (A.S) ya ce: kyauta tana dasa soyayya[38]. r- Kin sharri
80. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: wanda aka sanya masa kin sharri… Allah zai arzuta shi son mutane da faran-faran da su, kuma ya bar yankewa mutane da husumomi, kuma ba shi da komai tsakaninsa da wata husuma[39]. S- Barin Hassada
81. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: hakika ma’abocin addini… ya jefar da hassada sai kauna ta bayyana[40]. T- Kawar Da Kai daga Munana
82. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka kawar da kai daga munanan ayyukan ‘yan’uwa sai ka dawwamar da kaunarsu[41]. 5 / 3 Ayyukan Da Suke Kawo KaunarJuna
A- Fuskantar Da Zuciya Zuwa Ga Allah
83. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: matukar bawa ya fuskantar da zuciyarsa zuwa ga Allah, sai Allah ya sanya zukatan muminai suna karkata zuwa gareshi da so da kauna, kuma Allah ya kasance mafi gaggauta dukkan alheri zawa gareshi[42]. B- Fuskanta Da Zuciya A Cikin Salla
84. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: ni ina so ga mutum mumini daga cikinku idan ya tashi zuwa ga sallarsa ya fuskanto da zuciyarsa zuwa ga Allah madaukaki, kuma kada wani abu na al’amarin duniya ya shagaltar da shi; babu wani mumini da zai fuskanta zuwa ga Allah a sallarsa sai Allah ya fuskanta zuwa gareshi da fuskarsa, kuma ya fuskantar da zukatan muminai gareshi da so bayan kuma son da Allah yake yi masa[43].
|