Sabuban Soyayya57. Sunan ibn majah daga Abuzar Daga Manzon Allah (S.A.W) na ce masa: mutum yana aiki don Allah sai mutane su so shi a kan haka?! Sai ya ce: wannan shi ne albushir na gaggawa na mumini[16]. 4 / 3 Kyawawan Halaye Suna Kawo Kauna
A- Kyakkyawar Niyya
58. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: wanda niyyarsa ta kyautata, ladansa zai yawaita, kuma rayuwarsa ta dadada, kuma kaunarsa ta wajaba[17]. B- Kyakkyawan Zato
59. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: wanda zatonsa ga mutane ya kyautata, to zai samu kauna daga garesu[18]. C- Kyakkyawar Dabi’a
60. Imam Ali (A.S) ya ce: Kyakkyawar dabi’a tana sanya kaunar juna, kuma tana karfafa soyayya[19]. D- Kyakkyawan Zamantare
61. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: kyakkyawar abotaka tana dada kauna a zukata[20]. 62. Daga gareshi (A.S) ya ce: wanda ya kyautata abotaka, abokansa zasu yawaita[21]. f- Ikhlasin Kauna
63. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka tafiyar da al’amuran makiyinka, ka kuma yi ikhlasi ga masoyinka, ka kiyaye ‘yan’uwantaka kuma ka kare mutunci[22]. G- Sakin Fuska
64. Imam Ali (A.S) ya ce: Sakin fuska igiyar soyaya ce[23]. 65. Daga gareshi (A.S) ya ce: sakin fuska sababin soyayya ne[24].
|