Umar da Ra'ayin Shari'a 1



Amma imaman shiriya masu tsarki da masu bin su na imamaiyya sun yi ittifaki a kan cewa ‘yan’uwa da sauran dangi baki daya namiji ne ko mace, su na da yawa ko daya ne, ba su da wani abu matukar dai akwai da ko ‘ya ga mai gado ko da kuwa guda daya, suan masu kafa hujja da wannan ayar mai fadin Allah madaukaki cewa: “ma’abota kusanci sashen su sun fi cancanta da sashe” anfal: 75, kuma su na da magana mai tsanani kan sarayar dangi tare da samuwar da ko ‘ya daya daga gado ga wanda ya koma wa littattafansu na gado, kuma littafin wasa’ilus shi’a ya isa misali kan wannan, sai a koma.

Haka nan an tambayi dan Abbas game da mutumin da ya mutu sai ya bar ‘ya da ‘yar’uwa shakikiya, sai ya ce: ‘yar’uwarsa ba ta da komai, ‘ya ta na karbar rabi da gado, rabi kuma da raddi. Sai mai tambaya ya ce: Umar kuwa ya yi hukunci ba haka ba. Sai Ibn Abbas ya ce: Ku ne ku ka fi sani ko Allah?! Sai mai tambaya ya ce: Ban gane hakan ba. Sai da na tambayi Dawus game da wannan sai na gaya masa abin da Ibn Abbas ya ce, sai ya ba ni labara cewa: Babana ya ji labari cewa ya ji Ibn Abbas ya na cewa: Allah madaukaki ya na cewa: Idan mutum ya mutu ba shi da da kuma ya na da ‘yar’uwa to ta na da rabin abin da ya bari, sai ku kuma ku ka ce ta na da rabi ko da ya na da da[3].

 

 

Daga ciki, akwai aulun kason gado

Musulmi sun yi sabani a kan halaccin aulu ko rashin halaccinsa, hakikanin aulu shi ne a rage gado daga masu kaso kamar ‘yar’uwa biyu da miji, ‘yar’uwa biyu su na da sulusani, miji kuwa ya na da rabi, to sai lamarin ya rikece gun halifa na biyu wato Umar, ban san wanda zai gabatar ba, bai san wanda zai jinkirtar ba, sai ya yi hukunci da sanya ragi a kan dukkan kason.

Sai dai imaman shiriya (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) da malamai mabiyansu sun san wanda Allah ya gabatar sai su ka gabatar da shi, da wanda ya jinkirtar, sai su ka jinkirtar da shi.

Imam abu Ja'afar Bakir (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) yaan cewa: Imam Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya na cewa: Wannan wanda ya taskace yawan yashi, ya fi karfin sanin cewa kason gado ba ya wuce kaso shida da su na da basirar hakan.

Ibn Abbas ya na cewa: Wanda ya so zan yi mubahala da shi gun hajarul Aswad cewa Allah bai ambaci rabi guda biyu da sulusi ba a littafinsa, haka nan ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah mai girma, yanzu ku na ganin wannan wanda ya taskace adadin ya shi, ya kasa gane adadin har ya sanya dukiya rabi, da wani rabin da kuma sulusi, wannan rabin guda biyu sun tafiyar da dukiya, to yaya kuma wani sulusin daban zai samu? Sai aka ce amsa: Ya kai dan Abbas wane ne ya fara rage kaso ne? sai ya ce: Yayin da kason su ka ci karo da juna gun Umar, wasu su ka ture wasu kason, sai ya ce; wallahi ban san wanda Allah ya gabatar ba, ban san wanda ya jinkirtar ba, kuma ni ban samu wani abu da zai fiye maku ba sai in raba muku wannan dukiyar da nisbar adaddin dukiya. Ibn Abbas ya ce: Na rantse da Allah! Da ma kun gabatar da wanda Allah ya gabatar, kun jinkirtar da wanda Allah ya jinkirtar da ba a rage kason gago ba. Sai aka ce masa: Waye Allah ya gabatar, wa kuma ya jinkirtar? Sai ya ce: Duk wani kaso da ba shi da wani kaso sai daya kawai, to shi ne Allah ya gabatar, amma abin da ya jinkirtar shi ne duk wani kaso da ya ke gushewa daga kason sa to ba shi da komai sai abin da ya rage, wannan shi ne abin da Allah ya jinkirtar. Ya ce: Amma abin da Allah ya gabatar shi ne miji da ya ke da rabi, idan abin da ya ke mayar da shi zuwa ga rubu’I ya samu sai ya koma zuwa gare shi, haka nan mata da uwa duk su na da wannan (tashi daga wani kaso zuwa wani). Ya ce: Amma wanda Allah ya jinkirtar shi ne duk wani kaso kamar na ‘ya’ya mata da ‘yan’uwa mata da ta ke da rabi, da kuma sulusani idan sun wuce daya, idan gado ya kawar da su daga matsayinsu to ba su da komai sai abin da ya rage kawai. Ya ce: Idan abin da Allah ya gabatar ya hadu da wanda ya jinkirtar, sai a fara da wanda ya gabatar a ba shi gadon sa cikakke, sannan sai a ba wa wanda Allah ya jinkirtar ragowar dukiya. Wannan hadisin shahidus sani ma ya kawo shi a cikin Raudha. Ya ce: Mun kawo shi duka ne saboda ya na da abubuwa masu muhimmancin a cikinsa.

Na ce: Hakim ma ya fitar a cikin kitabul fara’idh shafin na 340 na littafinsa na mustadrak juzu’I na hudu, daga Ibn Abbas ay ce: Faron wanda ya rage kaso shi ne Umar, na rantse da Allah ina ma dai ya gabatar da wanda Allah ya gabatar, kuma ya jinkirta wanda Allah ya jinkirtar, da ba a rage kaso ba, sai aka ce masa: Waye Allah ya gabatar, wa kuma ya jinkirtar, sai ya ce: Duk wani kaso da Allah bai kawar da shi daga wani kaso ba, sai zuwa ga wani kaso to shi ne Allah ya gabatar kamar miji da mata da uwa, amma duk wani kaso idan ya kawu daga kasonsa ba shi da wani abu sai abin da ya ragowa to wannan shi ne Allah ya jinkirtar, kamar ‘yar’uwaye mata, da ‘ya’yaye mata, idan abin da Allah ya gabatar ya hadu da wanda ya jinkirtar sai a fara da wanda ya gabatar, sai a ba wa kowa hakkinsa cikakke, idan wani abu ya rage, to sai ya kasance na wanda ya jinkirtar ne… hadisi.

Don haka ne idan miji da uwa su ka hadu da ‘ya, sai a fara da miji da uwa a ba shi kason su hawa na biyu, wato rubu’I ga miji, sudusi ga uwa cikakku ke nan, sai kuma a bayar da ragowa ga ‘ya duka. Haka nan da ‘yar’uwa mata biyu za su hadu da su wadannan to ba su da komai ke nan, domin matakin gado gun imaman ahlul bait (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) guda uku ne kamar yadda ya ke kamar haka: Martaba na farko su ne iyaye maza da uwaye mata ban da iyayensu da uwayensu, da kuma ‘ya’ya maza da mata kamar yadda ya ke a littattafai, kamar miji da mata. Martaba ta biyu kuwa su ne: ‘ya’uwa maza da ‘yan’uwa mata da kakanni maza da mata, kamar yadda ya zo a bayani a littattafan fikihu. Martaba ta uku kuwa su ne: Ammomi maza da mata, da ‘yan’uwa uwa maza da mata kamar yadda ya ke a cikin hukuncin fikihu. Babu wata martaba ta kasa da za ta samu wani abu daga gado tare da samuwar martaba ta sama “ma’abota dangantaka wasu sun fi wasu cancanta daga cikinsu a littafin Allah” anfal: 75. Wannan kuwa shi ne abin da imaman shiriya su ka ta fi a kansa kamar yadda Allah da manzonsa su ka sanya a littafin Allah har zuwa ranar hisabi, kuma a kansa ne malaman shi’a imamiyya su ka yi ittifaki. Don haka ne za mu ga ‘yan’uwa mata biyu su na martaba ta biyu, don haka ba sa gado matukar akwai uwa a misalin da mu ka kawo.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next