Umar da Ra'ayin Shari'a 1Daga ciki: Karbar fansa daga ribatattun yakon badar
Yayin da Allah ya ba wa bawansa manzonsa nasara ranar da runduna biyu ta hadu a badar, kuma aka zo da ribatattun yaki wurinsa, sai aka san cewa ya yi nufin barin su rayayyu ne da fatan Allah ya shiryar da su a hannunsa daga baya ga addinsa, kuma ya sanya su masu dacewa ga abin da ya ke kira zuwa gare shi na tafarkinsa - kamar yadda hakan ya faru a tarijhi da godiyar Allah - wannan kuwa shi ne rahamar Allah (Mai Girma da Buwaya da Daukaka) da manzonsa (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ga bayi. Sai dai manzon Allah ya yi hukunci da yi musu afuwa da karbar fansa daga hannunsu domin ya raunata su daga yin gaba da shi, kuma ya samu karfi a kansu, wannan kwua shi ne ya fi zama maslaha ga dukkan bangareori biyu, kuma a cikin akwai tausayin Allah ga bayinsa kamar yadda ba ya buya cewa; "ba ya magana da son rai. Sai dai wahayi ne da aka yi" Najami: 3 - 4. Kuma ya kasance abin yi wa umarni da yin rahama ne, matukar akwai dammar yin ta. Kuma ya kasance ra'ayin Umar dan khaddabi shi ne a kashe su baki daya, sakamkon abin da su ka yi na karyata manzon Allah da cutar da shi, da nufin abin da ba su samu cimma burinsa ba, su ka fito su ka yi yaki, kuma ya kasance ya na da niyya mai tsanani ta cewa a kashe su ne ta hannun 'yan'uwansu na jinni daga musulmi har sai ya zama babu wani da ya rage daga cikinsu. Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi musu abin da ya ke shi ne abin da Allah ya ba mu labarin sa a cikin littafinsa mai daraja da daukaka na fadin nan na ubangiji madaukaki cewa: "Ba na bi sai abin da aka yi mini wahayi, ni ina jin tsoron azabar rana mai girma idan na saba wa ubangijina" Yunus: 15. Sai ya kyale su da afuwa da karamarsa, bayan ya riki alkawari a wurinsu na bayar da fansa, amma masu jahiltar isimarsa da hikimarsa bayan nan sai su ka kasance "… ba sa tashi sai dai kamar yadda wannan da shedan ya ke shafarsa saboda maye ya ke tashi, wannan kuwa saboda sun ce; hakika ciniki kamar riba ne, Allah kuwa ya halatta ciniki ya haramta riba, kuma duk wanda wa'azi ya zo masa daga ubangijinsa sai ya bari to abin da ya riga ya gabata nasa ne kuma lamarinsa ya na ga Allah ne, amma duk wanda ya sake komawa to wadannan su ne 'yan wuta su na masu dawwama a cikinta" Bakara: 275. Jahilan bayi masu mayen dimuwa su na cewa ni manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi ijtihadi ne a kayle su rayayyu da karbar fansa wurinsu[49], lamarin daidai shi ne ya kashe su, ya kawar da su, suan masu kawo hujja da hadisai kagaggu da babu hankali ko wahayi da zai yarda da su. Daga cikin wannan jahilcin akwai fadin su cewa Umar ya je wurin manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) bayan ya karbi fansa, sai ya tarar da shi ya na ku ka shi da Abubakar, sai ya ce: Me ku ke ku ka ne ni ma idan na samu abin ku ka ne sai in yi ku ka, in kuwa na kasa ku ka sai in rika kirkirar ku ka ni ma, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Azaba mai girma ta kusa fada mana saboda saba wa dan khaddabi, da azaba ta sauko da babu wanda zai kubuta daga cikiinta sai dan khaddabi[50], su ka ce: Sai Allah ya saukar da ayar nan cewa: "Ba zai yiwu ba ga wani annabi ya kasance ya na da ribatattun yaki har sai ya zubar da jinni a bayan kasa, ku ku na son rayuwar duniya ne, Allah kuwa ya na osn lahira, Allah mabuwayi ne mai hikima. Ba don wajabci ya rigaya ya gabata a wurin Allah ba (tun azal ya san cewa ba kama ayari ne zai kasance ba), da azaba mai girma ta same ku a sakamakon abin da ku ka rika" Anfal: 67 - 68. "Ba su girmama Allah matukar girmamawa ba" An'ami: 91. Yayin da su ka yi zurfi a dimuwa su ka halatta ijtihadi ga manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) alhalin Allah madaukaki ya na cewa: "Sai dai shi wahayi ne da aka yi" Najmi: 4. Kuma sun yi matukar zurfafawa cikin jahilci yayin da su ka jingina kuskure gare shi, su ka dulmuya cikin bata yayin da su ka fifita fadin waninsa, madafar sanin manufa ta rikice musu a wannan aya, mahangar shiriya ta bace musu da makantarsu, sai su ka ce ayar ta sauka domin ta yi gargadi ga manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) da sahabbansa ne, yayin da wadannan wawayen su ka raya cewa saboda ya so duniya ya fifita ta a kan lahira ne, sai su ka kama ribatattu su ka karbi fansa kafin su zubar da jinni, su ka raya cewa babu wanda ya kubuta daga kuskure a ranar nan sai Umar, kuma da azaba ta sauka da bai mai kubuta daga gare ta sai dan khaddabi. Duk wanda ya ce manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya kama ribatattu ya karbi fansa a wurinsu kafin ya zubar da jini to ya yi karya, domin kuwa manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi haka ne bayan ya zubar da jini a kasa, ya kashe manzon kuraishawa da dawagitansu kamar su abu jahal dan hisham, utba, shaiba dan abi rabi'a, Walid dan utba, asi dan sa'id, aswada dan Abul asad mahzumi, umayya dan khalf, zami'a dan al'Aswad, akil dan Aswad, nabih, munabbah, Abul bukhtari, hanzala dan abu sufya, du'aima dan udayyi dan nufar, nufar dan khuwaildi, haris dan zami'a, nadhar dan haris dan abdu dar, umair dan Usman ataimi, Usman da malik 'yan'uwan Dalha, mas'ud dan umayya dan Mugira, kaida dan fakh dan mugirak, huzaifa dan abi huzaifa dan Mugira, abu Kais dan Walid dan Mugira, amru dan makhzum, Abul munzir dan abi rifa'a, hajib dan sa'ib dan uwaimir, aus dan Mugira dan luzan, zaid dan malis, azim zan abi auf, sa'id dan wahab mai kawancen banu amir, mu'awiya dan abdul Kais, Abdullah dan jamil dan zuhair dan hariz dan asad, sa'ib dan malik, Abul hakam dan akhnas, hisham dan abi umayya dan Mugira… zuwa mutane saba'in daga manyan kafira da jagororin mushrikai kamar yadda aka sani, yaya kuwa bayan wannan lamarin wani zai ce ya karbi fansa kafin ya zubar da jini a bayan kasa da su na da hankali!? Yaya kuwa zai samu wannan zargi bayan kuwa ya zubar da jini ya ku musulmi?! Hakika manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya tsarkaka daga wannan zargi nasu tsarkaka mai girma. Abin da ya ke daidai a wannan ayyar shi ne; wannan ayar ta sauka ne ta na mai zargin wadanda sauka so a bi ayarin kasuwar mushrikai maimakon rundunar yakinsu kamar yadda fadin Allah madaukaki ya hakaito mana a fadinsa game da wannan yakin yayin da ya ke cewa; "Kuma yayin da Allah ya ke yi muku alkawarin dayan jama'a biyu cewa taku ce, ku kuma ku na son wacce ba ta da kaya ta kasance gare ku, kuma Allah ya na son ya tabbatar da gaskiya ne da kalmarsa ya yanke bayan kafirai" Anfal: 7. Kuma ya kasance manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi shawara da sahabbasa sai ya ce musu[51]: Mutanen sun fito a kan duk wata wahala da wuya sai sun gwabza me ku ke cewa? Ayari ku ka fi so ko kuma mayaka? Sai su ka ce ayari su ka fi soyuwa gare mu fiye da yakr makiya, wasu kuwa su ka ga ya dage a kan sai dai a yi yaki sai su ka ce: Ai da ka gaya mana kawai mu yi yaki da sai mu shirya? Mu mun fito ne don ayari ba don yaki ba, sai fuskar manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ta canja saboda bakin ciki, sai Allah ya saukar da ayar nan mai daraja madaukaki ya na fada: "Kamar yadda ubangijinka ya fitar da kai daga gidanka hakika wasu jama'a daga muminai su na ki. Su na jayayya da kai a game da gaskiya bayan ta bayyana gare su, kamar dai ana kora su ne zuwa ga mutuwa alhalin su na kallo" Anfal: 5 - 6.
|