Umar da Ra'ayin Shari'a 1
Wasu Abubuwa Da Umar Ya Saba Wa Nassin Shari’a Daga ciki, akwai sallar jana'iza
Manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya kasance yan ayin kabbara biyar ne ga janaza, sai dai halifa na biyu abin da ya kayatar da shi yin kabbara hudu ne, sai ya dora mutane kan yin kabbara hudu kawai, jama’a masu yawa daga malamai sun kawo wannan, daga cikin akwai suyudi yayin da ya kawo shi daga cikin abubuwan da Umar ay farar a littafinsa na tarikhul khulafa, da Ibn shahna yayin da ya kawo wafatin Umar a shekara ta 23 daga littafinsa na raudhatul manazir wanda aka buga a gefen littafin Ibn asir da waninsa na daga malamai. Haka nan ma da abin da ya zo a littafin demokradiyya na ustaz Khalid Muhammad Khalid daga abin da mu ka kawo dazu a babin saki uku. Haka nan Ahmad ya kawo a hadisin zaid dan arkam daga abdul’a’ala ya ce: Na yi salla bayan zaid dan arkam a wata janaza sai ya yi kabbara biyar, sai abu Isa Abdurrahman dan abu laila ya zo wurinsa ya kama hannunsa ya ce: Shin ka matan ne? ya ce: A’aha, sai dai ni na yi salla bayan Abul kasim manzon rahma (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) sai ya yi kabbara biyar, kuma ba zan bar su ba har abada[1]. Na ce: Zaid dan arkam ya yi salla ga sa’ad dan jubair da aka sani da sa’ad dan habta babarsa, shi ya na daga sahabbai ne, sai ya yi wa janazarsa kabbarori biyar, daga abin da Ibn hajar ya ruwaito a bayaninsa game da sa’ad a littafin isaba. Kuma Ibn kutaiba ya ruwaito shi a ahwali abu yusuf daga littafinsa na ma’arif, kuma wannan sa’ad shi ne kakan baban yusuful kadhi. Ahmad dan Hambal ya kawo a hadisin huzaifa ta hanyar yahaya da abdullahil jabir, ya ce: Na yi salla bayan Isa maulan huzaifa a mada’in ga wata janaza sai ya yi kabbara biyar. Sannan sai ya juya wurinmu ya ce: Ba na manta ba ne,ban gafala ba, sai dai ni na yi kabbara biyar ne kamar yadda shugabana mai yi mini ni’ima huzaifa ya yi ne, ya yi salla ga janaza sai ya yi mata kabbarori biyar, sannan sai ya juya wurinmu ya ce: Ban manta ba, ban gafala ba, sai dai ni na yi kabbara ne kamar yadda manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi kabbara[2]. Daga ciki, akwai shardanta gado tsakanin 'yan'uwa maza da 'yan'uwa mata, da cewa kada wanda za a gada ya zama ya na da da namiji
Allah madaukaki ya na cewa: “su na tambayar ka, ka ce Allah yaan ba ku amsa game da kalala () idan mutum ya mutu ba shi da da kuma ya na da ‘yar’uwa to ta na da rabin (1/2) abin da ya barik, shi kuma ya na gadon ta idan ba ta da da, amma idan sun kasance su biyu to su na da sulusani (2/3) na abin da ya barik, amma idan sun kasance ‘yan’uwa maza da mata ne, to namiji ya na da rabon mata biyu (na dukkan dukiya), Allah ya na yi muku bayani don kada ku bata, kuma Allah masani ne da komai. Nisa’i: 176. Wannan ayar ta shardanta gado tsakanin ‘yan’uwa maza da mata da sharadin kada ya kasance wanda za a gada ya na da da, kuma da a luga ya hada har da ‘ya. Sai dai Umar dan khaddabi ya dauki da a cikin wannan ayar da aka ambata da namiji kawai, sai ya sanya gadon tsakanin ‘ya mace da ‘yar’uwarta ta wajan uba da uwa, (shakikiya) ya sanya wa kowacce rabin abin da mai gado ya bari, sai masu mazhabobi hudu su ka bi shi a kan hakan.
|