Halayen Sayyida Zahara (s.a)Kuma abin da yake cikin sahihul buhari yana karfafa wannan lamarin cewa: أ¢â‚¬إ“daga Nafiأ¢â‚¬â„¢u cewa wani mutum ya zo wa Dan Umar sai ya ce; Ya baban Abdurrahman me ya sanya ka kake yin hajji wata shekara wata kuma ka yi Umara ka bar yaki saboda Allah madaukaki, kuma ka san cewa Allah ya kwadaitar game da shi? Sai ya ce: Ya kai dan danأ¢â‚¬â„¢uwana an gina musulunci a kan abubuwa biyar ne: Imani da Allah da manzonsa, da salloli biyar, da azumin watan Ramadhan, da bayar da zakka da hajjin dankin Allah. Sai ya ce ya kai baban Abdurrahman shin ba ka ji fadin Allah madaukaki a littafinsa ba: أ¢â‚¬إ“idan wasu jamaأ¢â‚¬â„¢a biyu na muminai suka yi fada ku yi sulhu tsakaninsu idan kuwa daya ta yi zalunci a kan dayar to ku yaki mai yin zalunci har sai ta koma zuwa ga alأ¢â‚¬â„¢amarin Allahأ¢â‚¬â€Œ (Hujurat: 9). أ¢â‚¬إ“Ku yake su har sai ya kasance babu wata fitina addini ya kasance na Allah neأ¢â‚¬â€Œ (Bakara: 193)? Sai ya ce: Mun yi wannan yayin da musulunci ya kasance kadan ne, ya kasance ana fitinar mutum daga addininsa ko su kashe shi ko kuma su azabtar da shi har sai da musulunci ya yi yawa babu wata fitina yanzu. Ya ce: me zaka ce game da Ali da Usman? Sai ya ce: Amma Usman Allah ya yi masa afuwa amma ku kuna kin yi masa afuwa, amma Ali shi dan Ammin Annabi ne kuma surukinsa, sai ya nuna gidansa ya ce: Wannan ne gidansa kamar yadda kuke ganiأ¢â‚¬â€Œ[12]. Ibn Umar yana nunawa da hannunsa zuwa ga gidan Ali (a.s) cewa; ya kasance tare da Annabi (s.a.w) kuma muna iya ganin yadda ya kawo cewa shi ne surukin Annabi (s.a.w) mijin أ¢â‚¬ع©yarsa amma bai fadi hakan ga Usman ba, wanda wannan yake nufin shi mijin agololinsa ne! Madogara: Masaأ¢â‚¬â„¢ilu Majallati JaishusSahaba; Alأ¢â‚¬â„¢ustaz Ali Kurani Alamili أ¢â‚¬ع©Yar Annabi (s.a.w) Fadima Zahara (a.s)
Ita ce Fadima Zahara (a.s) kuma babanta shi ne Muhammad dan Abdullahi, kuma babarta ita ce sayyida Hadiza uwar muminai, mijinta shi ne Imam Ali shugaban wasiyyai, kuma daga 'ya'yanta da jikokinta akwai imamai masu tsarki. An haifi Fadima ishirin ga jimada sani a shekara ta arba'in daga rayuwar Annabi (s.a.w) kuma ta yi shahada tana abar zalunta a ranar talata uku ga jimada sani shekara ta sha daya hijira, shekarunta goma sha takwas ne. Imam Ali (a.s) shi ne ya binne ta a Madina ya boye kabarinta da wasiyyarta domin ta kafa hujja kan al'umma da zaluntar ta da aka yi da kuma kwace mata hakkinta. Kuma ta kasance kamar babanta a ibada da zuhudu da fifiko da takawa, kuma Allah madaukaki ya saukar da ayoyin Kur'ani game da ita[13].
|