Halayen Sayyida Zahara (s.a)Wannan al'amarin kawai ya isa ga mai karatu ya yi tunani a kai, me ya sa haka ta faru In ba dalili, me ya sa yanzu ba wani mahaluki cikin al'ummar annabi (s.a.w) da zai iya zuwa Madina ya ce ga barin 'yar Manzon Allah?! Bayan haka mata kabari ne, sai Imam (a.s) ya shiga cikin kabarin sannan Abbas da dansa Fadhal suka mika mishi ita ya sanya ta cikin kabarin. Hawaye suna ta zubo masa bi da bi! Bayan ya sanya ta sai ya ce: "Ya kasa ga amana nan na ba ki, wannan ita ce diyar Manzon Allah, da sunnan Allah Mai Rahma, Mai jinkai, da sunan Allah bisa addinin Manzon Allah! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com www.hikima.org Saturday, July 31, 2010
|