Halayen Sayyida Zahara (s.a)Sai Manzon Allah (s.a.w) ya yi kuka kuma duk wanda yake tare da shi a cikin gidan ya yi kuka, Fadima ta rankwafa ta shiga cikin lullubewar uban (s.a.w) kamar yanda أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yan kaza suke shiga cikin fukafukan babarsu, kalma ce da tafi abin da ya faru ciwo saboda bakin ciki ne ya sami uwa da take tafi uwa kima domin ita uwa ce daga bakin wahayi daga duniya mai tsarki da nisa daga duniyar أ¢â‚¬ع©yan mariskai, da wannan maأ¢â‚¬â„¢ana ta duniya da ba mai gane hakikanin maأ¢â‚¬â„¢anarta sai masu ilimi. Ya girman nauyin wannan tambaya a wannan hali mai wahala da bakin ciki daga gareta (a.s)!! Saboda haka sai fiyayyen halitta (s.a.w) ya fada yana mai lallashin halinta da neman kawar da nata bakin cikin da ba bakin cikin da ya kai shi ciwo da zafi, ina iya cewa: bakin cikin da yake ji sai ya ta fi sakamakon ganin halin da take ciki, saboda haka sai hadafinsa ya zama shi ne kokarin kawar da nata bakin cikin yana mai fada da harshe mai laushi da taushin murya domin sanyayawa ga zuciyarta: "'Yata hakika Babarki ta tafi aljanna kuma hakika danأ¢â‚¬â„¢uwana Jibril (a.s) ya ba ni labari cewa tana nan a wani gida na karau ba wahala ba hayaniya a cikinsa[6]". Haka nan Fadima ta zama marainiya ba uwa, ta samu daci a rayuwa tana أ¢â‚¬ع©yar shekara takwas dacin da ba ta tada samun irinsa ba sai a lokacin wafatin Babanta (a.s). Haka nan aka gaggauta mata fitunu da jarabawowi a rayuwa a shekaru na budurci har zuciyar ta ta tsage saboda rashin uwa!! Bakin ciki ya girgiza ta tana karama mai rauni, ta kusa ta fadi kasa ba don juyawa da Baban (s.a.w) ya yi zuwa gare ta ba da gaggawa yana mai shafe mata hawaye kamar yadda take shafe masa, ta kafu a kan hakuri da juriya!!. Tana mai dimuwa cikin lamarinta, ba ta san mai zata yi ba; shin zata yi juriya ne da balaأ¢â‚¬â„¢in da ya same ta na rashin uwar da babu wata uwa kamarta ko kuma zata yi wa Babanta da babu uba kamarsa taأ¢â‚¬â„¢ziyyar rashin matarsa da babu wata mata kamarta ne!. Nan da nan sai ta zabi ta kasance mai taأ¢â‚¬â„¢aziyya da lallashi ga uban domin bazatar da aka yi masa na amminsa da matarsa, tana mai yakini cewa ba ya rasa mata maras misali ne kawai ba, har ma ya rasa mai kariya ne mai dauki-ba-dadi da gwagwamarya domin kare hadafinsa kamar yadda amminsa Abu Talib (a.s) yake daya rukunin mai kare shi mai kuma lallashi da tausayi mai juriya, kuma ga shi ya rasa masu ba shi kalmomi masu dadi da raأ¢â‚¬â„¢ayi mai dacewa. Sai Fadima ta yunkura ta motsa a wannan karon ba domin ta tambayi Babanta ba sai domin ta lallashe shi ta kara masa karfin gwiwa ta kawar da bakin cikinsa tana mai shafe masa hawayi daga kumatunsa masu albarka (s.a.w) tana nuna masa kauna irin wacce uwa kan nuna wa danta da kuma son nan da ya rasa daga Khadiza, domin haka ne ta zama Babar banta kuma أ¢â‚¬ع©yarsa a lokaci guda[7]. Haka nan ta zama uwa ga uban (a.s) a kiyayewa da kauna kuma أ¢â‚¬ع©ya a nasaba da tarbiyyatarwa da koyi amma uwa a kula da kiyayewa. Haka nan ta fara wata marhala ta rayuwa sabuwa ta fara sabon shafi na rayuwa da Babanta ko zata iya zama kamar khadija ga Babanta (s.a.w) kamar yadda Ali (a.s) ya zama kamar amminsa (s.a.w) Abu Talib (a.s) gareshi.
|