Halayen Sayyida Zahara (s.a)



Ita ce tsokar jikin Manzon Allah (s.a.w), don haka ne dukkan halayensa su ne halayen sayyida Zahara (a.s), kuma hatta da tafiyarsa da maganarsa ba su da bambanci da yadda Manzon Allah (s.a.w) yake yin nasa.

Ta kasance ita ce ta fi kowa ibada bayan babanta da mijinta, domin tana tashi har sai kafafunta sun tsattsage, har ma tana kwana tana ibaba ba ta komai sai ambaton Allah da yi wa makota da alأ¢â‚¬â„¢ummar musulmi adduأ¢â‚¬â„¢oأ¢â‚¬â„¢I, hatta da danta Hassan (a.s) yana cewa: أ¢â‚¬إ“Ya baba! Kin kwana kina salla amma ban ji kin yi wa kanki adduأ¢â‚¬â„¢a ba sai dai makota? Sai ta ce masa: Ya dana; Makoci sannan gida!.

Wannan ita ce Fadima (a.s) mai ibada da zuhudu, da kin zalunci, da tsoron Allah, da kame kai, da kuma kariya ga alأ¢â‚¬â„¢umma, da neman kafa adalci, da yin tsaye gaban duk wani zalunci.

Salman Muhammadi ya ga faci goma sha biyu a jikin kayanta na gashin tumaki sai ya fashe da kuka yana cewa: أ¢â‚¬ع©Yaأ¢â‚¬â„¢yan sarkin Rum da na Farisa suna cikin alhariri da sundus, amma أ¢â‚¬ع©yar Muhammad annabin Allah (s.a.w) tana cikin tufafi masu kaushi kuma da fashi goma sha biyu!?

Ta kasance tana yin nika da hannunta har sai suna kumbura suna yin ruwa, kuma tana shayar da أ¢â‚¬ع©yaأ¢â‚¬â„¢yanta da kanta, tana sanya tufafin da aka yi da fatar rakuma, babanta mai tsira da aminci ya gan ta a wannan halin sai ya ce: Ya أ¢â‚¬ع©yata ki gaggauta dacin duniya da zakin lahira. Sai ta ce: Ya Manzon Allah, godiya ta tabbata ga Allah kan niأ¢â‚¬â„¢imominsa da gode masa a kan baiwowinsa.

Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana fara tafiyarsa da yin bankwana da ita ne, kuma idan ya dawo yana fara shigowa cikin madina da zuwa wurinta ne. Wata rana saboda tarbarsa ta taba sanya wani tufari na Khaibar domin tarbar babanta da mijinta. Yayin da Manzon Allah (s.a.w) ya ga hana sai bai ji dadi ba, da ta fahimci haka, sai ta cire sarkarta da dan kunnenta, da kayan da ta sanya ta aika masa da shi ta ce; ya sanya shi a cikin tafarkin Allah. Yayin da ya ga haka sai ya tausaya mata ya ce: Ta yi abin da ya fi kyawu, babanta fansa ne gareta har sau uku, sannan ya ce: Babu ruwan alayen Muhammad da duniya, domin su an halicce su ne don lahira, an kuma halicci duniya don su ne. A wata ruwayar akwai karin ya ce kuma: Wadannan su ne alayena, ba na son su ci mai dadinsu tun a rayuwarsu ta duniya.

Fadima (a.s) ta kasance matukar gaya wajen ilimi, ta kasance tana amsa tambayoyi cikin sauki, hatta da tambayar da Manzon Allah (s.a.w) ya tambayi sahabbansa game da cewa أ¢â‚¬إ“mene ne ya fi cancanta ga maceأ¢â‚¬â€Œ wata rana suka kasa amsawa sai ita ce ta gaya wa mijinta amsa cikin sauki, shi kuwa ya zo ya gaya wa Manzon Allah (s.a.w) abin da ta ce.

Ta kasance makoma gun mata da maza kan masأ¢â‚¬â„¢alolin addini, don haka ne ba ta da iyaka ga dukkan mai koma mata don neman amsar tambayarsa. Sannan an ruwaito hadisai masu yawa daga gareta tsira da amincin Allah su tabbata gareta.

 Wata mata ta taba zuwa wurinta ta tambaye ta masأ¢â‚¬â„¢aloli goma ita kuma tana amsawa, sai matar ta ji kunyar ci gaba da tambaya tana ganin kamar ta tsawaita mata, matar ta ce: Bana son in wahalar da ke da takurawa. Sai Fadima Zahara (a.s) ta ce: Ki tambayi duk abin da kike so, ki sani, ni na ji babana (s.a.w) yana cewa: أ¢â‚¬إ“Hakika malaman alأ¢â‚¬â„¢ummata ana tayar da su, sai a rika ba su girma daidai gwargwadon yawan iliminsu, da kokarinsu na shiryar da bayin Allahأ¢â‚¬â€Œ.

Ta kasance mai tsananin fasaha matuka, Aأ¢â‚¬â„¢isha tana cewa: Ban taba ganin wani wanda ya fi kowa kama da Manzon Allah (s.a.w) a magana da zance ba da ya kai Fadima (a.s). Duk wani wanda ya san hikima ya duba hudubarta to zai san kimarta da kimar maganganunta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next