Mutum Mai KamalaWanene Muhammad (S.A.W)
Muhammad shi ne annabin da Allah a aiko shi a matsayin annabin karshe domin shiryar da dukkan halitta gaba daya. A lokacin da aka haife shi Makka da Dakin Allah sun kasance a cike da daudar bautar gumaka, sannan kuma Yahudawa da Kiristoci suna rayuwa a Jazirar larabawa. Daular Farisa tana mallakar gabashin jazirar larabawa, kuma ga daular Rumu a yammacinta maso arewa, kuma da daula ta uku ta Habasha a yamma, kuma a kudu akwai Daular Yemen da ta kasance karkashin mulkin mallakar Habasha a lokacin haihuwar annabi, da kuma Tekun Indiya. An ambaci shekarar haihuwarsa da “Shekarar giwaâ€, saboda harin da Habasha ta kai wa Ka’aba domin rusa ta a wannan shekarar. Kuma abubwan mu’ujiza sun wakana yayin haihuwarsa (S.A.W) da suka hada da: 1. Faduwar gumaka akan fusakunsu 2. Rushewar katangun kisira da suke Shiraz 3. Mutuwar wutarsu da suke bautawa 4. Kafewar kogin Sawa a. Dukkan wadannan abubuwa sun faru ne a shekarar miladiya ta 571 ne. Babarsa ita ce Amina ‘yar Wahabi (A.S)
|