Mutum Mai Kamala



Ashe ba jingina kaskanci da wauta ba ne ga mafificin halitta gaba daya, mafi hikimarta, mafi iliminta, wasu musulmi suke yi ba da suke jingina rashin barin halifa ga Manzo (S.A.W) wanda zai tsayu da irin wadannan al’amuran da muka lissafo da ma wasunsu masu yawa.

Idan ya kasance Manzon rahama (S.A.W) ba ya iya barin Madina koda na dan lokaci kankani ba tare da ya ayyana wani mai kula da ita ba, ashe zai yiwu ya san cewa zai bar duniya gaba daya sannan sai ya zamanto bai ayyana wa al’umma wanda zai maye gurbinsa ba! Don haka ne bisa hikimar Allah madaukakin sarki tun farkon kiransa yake shaidawa da cewa yana da wasiyyi a wurare masu yawa da suka zo a ruwayoyi gun Ahlul Bait (A.S) da kuma daga ‘yan’uwanmu Ahlussunna, wanda wasu daga cikin wadannan ruwayoyi suna masu kawo sunansa wato imam Ali (A.S).

Don haka ne ma cikin hikimar Allah bayan hajjin bankwana sai ya umarci Manzo da ya karbi bai’ar musulmi ga imam Ali a matsayin halifansa bayansa tun yana raye, domin wannan ya zama hujja a kan musulmi da duniya gaba daya, kuma Allah ya cika haskensa da ni’imarsa garesu da wilayar imam Ali da Ahlul Bait (A.S) bayan Annabin rahama (S.A.W).

Saboda haka sai Manzo (S.A.W) ya umarci a tara mutane bayan sun fito daga Makka a lokaci mai zafin rana, kuma ya yi umarni da a dawo da wadanda suka yi gaba; suka yi nisa, kuma a jira wadanda ba su iso ba a wani waje da ake kira KHUM. Game da irin wadannan matakai da ya dauka masu tarihi suna cewa; ya dauke su ne domin muhimmacin al’amarin kuma da hikimar ya zama ya wanzu a kwakwalen mutane ne.

Bayan jama’a sun taru ne ya sa aka kafa wani mimbari ta yadda kowa zai ji shi, kuma ya gan shi, sannan sai ya hau kan mimbarin ya yi huduba mai tsayi, daga cikin abin da wannan huduba mai tarihi ta kunsa ya zo kamar haka:

Aka tara mutane aka yi masa minbari sannan sai annabi (S.A.W) ya hau kansa bayan ya yi salla a cikin wanan taron na musulmi sannan sai ya godewa Allah ya yabe shi, ya fada da sauti madaukaki da duk wanda yake wajan yana jin sa: “Ya ku mutane! Ya kusata a kira ni sai in amsa, ni abin tambaya ne, ku ma ababan tambaya ne, me zaku ce? Suka ce: Mun shaida ka isar da sako ka yi nasiha, ka yi jihadi, Allah ya saka maka da alheri. Ya ce: Ba kuna shaidawa cewa babu wani ubangiji sai Allah ba, kuma Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, kuma cewa aljanna gaskiya ce kuma alkiyama mai zuwa ce babu kokwanto a cikinta, kuma Allah yana tayar da wanda suke cikin kaburbura? Suka ce: Haka ne mun shaida da hakan. Ya ce: Ya ubangiji ka shaida. Sannan ya ce: Ni zan hadu da ku a tafki, kuma ku zaku zo mini a tafkin, wanda fadinsa ya kai tsakanin San’a’a da Busra, a ciki akwai kofuna na azurfa sun kai yawan taurari, ku duba ku gani yaya zaku kusance da alkawura biyu masu nauyi bayana”.

Sai wani ya daga murya yana mai tambaya; ya Manzon Allah (S.A.W) menene alkuwura biyu masu nauyi? Manzon Allah ya ce: Alkawari mafi girma shi ne Littafin Allah, gefensa a hannun Allah daya gefen a hannunku, ku yi riko da shi kada ku bata, dayan kuma mafi karanta su ne Ahlina (Ahlul Bait). Hakika (Ubangiji) mai tausayi mai sanin komai ya bani labari cewa; ba zasu taba rabuwa ba har sai sun riske ne a tafki, kuma na roka wa abububwan nan biyu wannan a wajan ubangijina. Kada ku shiga gabansu sai ku halaka, kuma kada ku takaita gabarinsu sai ku halaka”.

Sannan sai ya yi riko da hannun Ali dan Abu Talib (A.S) har sai da aka ga farin hammatarsu, mutane suka san su gaba daya. Sai Manzo ya ce: “Ya ku mutane wanene ya fi cancantar biyayyar muminai fiye da kawukansu? Suka ce: Allah da Manzonsa su ne mafi sani. Ya ce: Ubangiji shugabana ne, kuma ni ne shugaban muminai, kuma ni na fi cancanta da biyayyar muminai fiye da kawukansu, to duk wanda nake shugabansa wannan Ali shugabansa ne”, yana maimaita wannan har sau uku.

Sannan sai ya ce: “Ya ubangiji! Ka jibanci lamarin wanda ya bi shi, ka ki wanda ya ki shi, ka so wanda ya so shi, ka kyamaci wanda ya kyamace shi, ka taimaki wanda ya taimake shi, ka tabar da wanda ya bar shi, ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya, ku sani wanda ya halarta ya isar wa wanda bai halarta ba”.

Sannan jama’a ba ta watse ba har sai da Jibrilu ya sauka da wahayin Allah da fadinsa: “Yau ne na kammala addininku gareku, kuma na cika ni’imata a gareku, kuma na yarda da musulunci addini gareku”[12].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 next