Mutum Mai KamalaBayan wannan hijira ta farko zuwa Habasha ne da jagorancin Ja’afar dan Abu Talib (A.S) sai kuraishawa suka yi kokarin dawo da su daga wajan sarkin Habasha amma ba su ci nasara ba, al’amarin da ya ba su haushi suka sanya takunkumi mai zafi kan Bani Hashim da ya yi sanadiyyar mutuwar Abu Talib da sayyida Khadiza (A.S) a wannan yanayi mai wahala da yunwa da kunci, har manzo (S.A.W) ya kira shekarar mutuwarsu da “Shekarar bakin cikiâ€. Amma bayan shekara uku da wannan takunkumi mai muni na hana saye da sayarwa, da mu’amala, da auratayya, da sanya hannun jagorori arba’in na Kuraishawa da aka kakaba musu ne sai Allah ya sanya gara ta cinye rubutun wannan mummunan takunkumi da aka rubuta aka rataya a dakin Ka’aba, ba abin da ta bari sai kalmar “Bismikallahumm†wato Da sunanka ya Allah!. Hijira Zuwa Madina
Bayan karewar lokacin takunkumin da aka kakaba wa Manzo (S.A.W) a sakamakon rasa kariya biyu masu girma da ya yi; wato kariyar tattalin arziki daga Khadiza (A.S) da kuma kariya daga sharrin al’umma daga Abu Talib (A.S) sai kuraishawa suka samu damar wulakanci da takurawa ga Manzo (S.A.W) da damar da ba su taba samun irinta ba, har ya kasance Manzo Muhammad (S.A.W) yana cewa: “Kuraishawa ba su taba samu dama a kaina da abin ki ba sai da Abu Talib ya rasuâ€. A sakamakon haka ne Manzo (S.A.W) ya fuskanta zuwa ga kabilun larabawa na garuruwa daban-daban domin neman masu amsa wannan kira domin ya koma zuwa garesu, har ya kai zuwa garin Ta’ifa amma bai samu abin da yake so ba, sai mutanen garin suka yi masa isgili suka jefe shi da duwatsu, wannan al’amari ya sanya shi komawa Makka domin cigaba da haduwa da kabilun larabawa da suke zuwa aikin hajji, a nan ne ya hadu da mutane bakwai daga kabilar Khazraj da take rayuwa a Madina. Mutanen Madina sun yarda da shi a matsayin Annabin da suka ji yahudawa suna ba su labarin zai bayyana, don haka a shekara mai zuwa sai suka zo su goma sha biyu ya kuma aika Mus’ab dan Umair tare da su domin ya sanar da su musulunci, wannan al’amari ya sanya yaduwar musulunci a cikinsu. Bayan yarjejeniyar hijirar Annabi (S.A.W) zuwa Madina sai Kuraishawa suka hada mutane arba’in daga kowace kabila ta larabawan Makka domin su kashe Annabi ta yadda Banu Hashim ba zasu iya daukar fansan kisansa ba sai dai su yarda da diyya. Wanann al’amari ya sanya ya bar wasiyyinsa Ali dan Abu Talib (A.S) a kan gadonsa domin su dauka Annabi yana nan, sai suka kwana suna ganin sayyidi Ali (A.S), kamar yadda ya bar masa iyalansa domin ya yi hijira tare da su; wato Fatima ‘yarsa, da kuma Fatima ‘yan Asad babar imam Ali (A.S), da kuma Fatima ‘yar Zubair, da kuma dukkan wanda yake son hijira tare da shi na daga Banu Hashim. Manzo (S.A.W) ya jira imam Ali (A.S) a Kuba’a har sai da ya zo sannan suka shiga Madina su biyu tare da iyalansa, kuma aka yi musu tarba mai girma, da wannan ne aka kafa tushen hukumar musulunci ta farko a Madina karkashin jagorancin Manzon rahama (S.A.W). Annabi (S.A.W) A Madina
Manzon Allah (S.A.W) ya isa Kuba’a a 12 ga watan rabi’ul awwal, sannan ya jira zuwan imam Ali (A.S) tare da Fatimomi kamar yadda ya gabata da kuma Ummu Aiman, Manzon Allah ya tarbi imam Ali (A.S) kafafuwan imam Ali suna zubar jini saboda nisan tafiya, kuma ya gina farkon masallaci a Kuba’a, sannan bayan kwana goma sha biyar ya fuskanci Madina, ya shiga Madina a ranar jumma’a, mutanen Madina suka tarbe shi suna masu farin cikin zuwan wannan shugaba da ba shi da tamka. Ya zauna tare da iyalansa da imam Ali (A.S) a gidan Abu Ayyub wata daya har ya gina masallacinsa na Madina, amma sauran muhajirun da suka zo daga Makka mutanen Madina sun yi wawason su zuwa gidajensu. A cikin wannan yanayin Manzon Allah (S.A.W) ya fuskanci manyan kalubale guda uku da suke matsala ta asali a Madina: 1. Yahudawan Madina da na wajanta wadanda suke da dukiya mai yawa
|