Mutum Mai Kamala



2.     Sabanin da yake tsakanin muhajirun da ansar da kuma tsakanin su ansar kansu

3.     Kuraishawa da sauran mushrikai masu rayuwa a yankin larabawa gaba dayansu

Amma Manzon rahama da hikimarsa (S.A.W) ya yi kokarin warware wadannan matsaloli dukkansu gaba daya ta hanyoyi masu hikima.

1.     Ya warware matsalar Yahudawan Madina da na wajan Madina kamar Banu Kuraiza, da Banu Kainuka’a, da Banu Nadir, ta hanyar rubuta takardar zamantakewa tsakaninsu da sauran musulmi da rashin cutar da juna, sai dai Yahudawa sun karya wannan yarjejeniya daya baya daya kamar yadda ya zo a tarihi, al’amarin da ya sanya aka hukumta su daidai abin da sharuddan yarjejeniya suka tanada.

2.     Ya warware matsalar Aus da Khazraj ta hanyar kulla ‘yan’uwantaka tsakaninsu da kuma ‘yan’uwantaka tsakanin Ansar da Muhajirun banda imam Ali (A.S) da Manzo (S.A.W) ya ce da shi: “Ya Ali! Kai dan’uwana ne a duniya da lahira”.

3.     Amma matsalar Kuraishawa da sauran mushrikai da sukan kawo hari ga daular musulunci Manzo ya fuskance ta da raddi ne da kuma kariya ga wannan daula sabuwa.


Yakokin Manzo (S.A.W)

Kiran Manzo (S.A.W) bai zo domin ya yadu ta hanyar yaki da takobi ba, sai dai yanayi ne ya tilasta haka domin kuraishawa da sauran mushrikai sun kai hari iri-iri a kan Manzo da musulmi ta hanyoyi daban-daban, kamar ta hanyar tattalin arziki, da siyasa, da nuna karfin yaki. Wannan al’amari ya tilasta wa Manzo (S.A.W) daukar mataki domin kare daular musulunci da jinin musulmi, al’amarin da ya kai ga yake-yake a lokuta daban-daban, mafi muhimmancin yakokin Annabi (S.A.W) kamar yadda suka zo a tarihi su ne:

·        Badar

·        Uhud

·        Banu Nadir



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 next