Hakkoki A Musulunci



Amma a tsari na adalci dole ne shugaba ya ji cewa shi daya ne daga cikin ‘ya’yan al’ummarsa, wannan zan sanya idan ta gan shi ta nuna shaukinta da kaunarta gareshi, idan ya mutu tana nuna bakin cikinta kamar yadda a wannan zamani namu ya faru ga Imam khomaini da mutane sama da miliyan ishirin suka zo jana’izarsa, mutanen kasarsa suka yi kwanaki suna kuka, kasar gaba dayanta ta shelanta zaman makoki na kwanaki. Ta haka ne a kan gane waye ya yi wa al’ummarsa adalci? Waye kuma ya zalunce ta?

Akwai wanda ya taba rike babban mukami a kasar nan amma da ya mutu mutane da yawa sun yi bukukuwan murnar mutuwarsa, aka hole aka yi annashuwa, a kan titina. Akwai kuma wadanda suka mutu amma har yanzu al’umma tana bakin cikin rashinsu, wannan kuwa ya isa wa’azi ga na yanzu rayayyu.

Hakkin Shugaba A Kan Al’umma

Daga cikin hakkokin shugaba su ne; a yi masa biyayya ga abin da bai saba wa Allah (S.W.T) ba. Kuma wasu bayanai sun zo game da cewa; yana daga hakkin shugaba a kan al’umma a ba shi shawara da nasiha, idan kuwa zai kauce hanya sai a tuna masa, sannan a taimaka masa domin ci gaban addini da al’umma gaba daya[36].

Dan kasa na gari shi ne wanda yake kiyaye doka koda kuwa ta kan titin mota ce. Wani malamin Ilimin tafiyar da al’amuran al’umma ya taba ba mu labari cewa: Wata rana ya dauko wani dalibinsa suna tafiya, sai suka isa wata danja ba mota ko daya amma bangarensu ba a bayar da hannu ba sai ya wuce. Sai dalibinsa ya ce: Amma da an kiyaye. Sai ya ce da shi: Ai ba mota. Sai dalibin ya ce: Amma da ka girmama dokar da kuma wadanda suka sanya dokar, don sun yi tunani kafin kafa ta, kuma don maslahar kanka da ta sauran ‘yan kasa ne. Ya ce: Sai ya yi kwana ya koma ya sake jira sannan ya wuce. Tun ran nan ya amfana da nasihar dalibinsa kuma ya yi masa godiya.

Hakkokin Dan Kasa A Kan Shugaba

Yana daga cikin hakkokin dan kasa a samar masa da aminci, da kariya, da lafiya, da ilimi, da hakkin fadin ra’ayinsa, da hakkin zamantakewa, da na walwala, da dukkan abin da ya shafi ci gaban rayuwarsa ta Duniya da Lahira. Haka nan yana da hakki kan masu tsaron kasa, amma wani abin haushi shi ne; samun tazara mai yawa tsakanin masu tsaron kasa da al’umma, ta yadda al’umma ba ta ganinsu wani bangare nata. Wannan kuwa yana faruwa ne sakamakon ba sa ji ko kadan cewa suna aiki don al’ummarsu ne kamar suna aiki don shugaba ne.

Wannan mummunan kuskure ya sanya masu kare doka sai su yi zalunci babu tausayi, har ma takan kai ga lahantawa ko salwantar da rai, kuma ga karbar cin hanci da ya zama ruwan dare. Koda yake a ciki akwai mutane masu hankali da kula da aiki da son taimakon al’umma kuma ba sa karbar cin hanci, irinsu ne suke iya mutuwa wajan kare mutanensu, amma da yawa ba haka suke ba sai dai kokari wajan neman na aljihunsu kawai sun manta da manufarsu. Wani lokaci kamar suna cike da jin haushin mutane ne, ta yadda da sun kama mai laifi sai duka da azabtarwa, alhali shi mai laifi koda kuwa barawo ne da makamancinsa mai kare doka ba shi da hakkin yi masa wani abu sai dai ya kai shi kotu ta yanke masa hukunci.

Ban taba sanin cewa al’umma tana da tazara mai yawa da ‘yan doka ba sai ranar da na samu nawa rabon, har ma wani yana jinginamu da wata kasa kai ka ce su ba mutane ba ne. Wani daga cikinsu ya ce: Irin wannan ku rika guduwa tun da ku ba ma su laifi ba ne! Kai ka ce su makafi ne da ba sa ganin mai laifi!. A ofishinsu ne na ga wani ana ta dukansa wai ya yi taurin kai a shiga mota, ana buga kansa da kasa, shi kuwa yana ta la’antar duk wani uba ko uwa na dan sanda.

Kuma a nan ne na yi mamakin yadda wani tsararre yake la’antar uwar ma da ta haifi dan sanda, har ma ya ce: Babansa ya taba cewa da shi tun da ya rasa aiki ya yi aikin dan doka. Sai ya ce: Ai baba gwara ka tsine mini in san ni tsinanne ne da in yi wannan aiki, ya kara da cewa: Wallahi in gawa ta kai dubu to shi zai iya gano ta dan sanda a ciki don fuskarsa ba ta cikawa da imani.

A lokacin ne na san cewa lallai akwai tazara mai yawa sosai tsakanin ‘yan sanda da al’umma, amma ra’ayin mutane da yawa ya tafi a kan cewa: Zafin zalunci da take hakkin dan Adam shi ya jawo haka, ta yadda mai tsaron kasa yake ganin yana yi wa shugaba aiki ne ba al’ummarsa ba, kuma yana ganin hadafinsa shi ne ya huce haushinsa kan al’ummarsa, sai ya cire wa al’umma jin cewa shi daga cikinta yake.

Haka al’amarin yake game da soja, kamar yadda dan sanda yake da hakkin kare cikin kasa da samar da aminci, haka ya zama wajibi a kansa ya kare kasa daga waje kada wani ya kai farmaki kanta. Amma wani abin takaici al’umma ba ta jin su nata ne haka su ma ba sa jin al’umma ta su ce. A misali da za a yi rigima tsakanin wani dan kasa da soja, da zaran sojoji sun isa wurin ba sa tambaya, a wurinsu mai gaskiya shi ne mai kaki na soja. Wannan rashin ganin juna a matsayin abu daya ya shafi har matsayin auratayya, domin na sha jin soja (ladani ne) yana nasiha a masallacin Barikin Bukabu da yake Kano yana cewa: Me ya sa ba a zuwa daga gari a auri ‘ya’yansu? Ko su ba kamar sauran mutane suke ba. Haka nan aka jahilci hakkin juna tsakanin mai tsaro da wanda ake tsaro har ya zama kamar al’umma daban-daban ce a cikin al’umma daya.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next