Hakkoki A Musulunci



Haka nan ba ya halatta ga mutum ya halakar da ransa ta kowace hanya, kamar ta hanyar ganganci da mota ko babur da kowane irin abin hawa da zai iya kaiwa ga cutar da jiki, ko kin shan magani ga maras lafiya.

Haka nan ji da gani, da hannu, da ciki, da kafa, da farjinmu, duk suna da hakki a kanmu na kada mu yi sabo da su, kuma mu nemi Duniya da Lahira da su, kuma mu nemi Ilimi da su ta hanyar gani, da ji, da tafiya wajan neman Ilimi ko neman halal, haka nan kada mu taba haram ko daukarta ko kallonta da su. Wani lokaci ana zaluntar kai ne da zaman banza har ma kana iya ganin mutum ya shantake yana ta barci wai hutawa yake yi saboda lalacewa alhali bai yi aikin komai ba. Wani kuwa yana alfahari ne da cewa babansa yana da dukiya mai yawa, sai ya zalunci kansa ba zai je ya nemi abin da zai mutunta kansa ba.

Hakkin Kiyaye Harshenmu

Ya zo a ruwayoyi cewa harshe mai dadi da kalma ta alheri sadaka ne[60], kuma ya zama wajibi a kare shi daga maganganu na karya, da hada husuma, da giba, da annamimanci. Kalma mai dadi da harshe mai hada sulhu tsakanin mutane[61] shi ne wanda Allah ya ke so. An karfafa yin hakan musamman tsakanin ma’aurata da abokan zamantakewa a matsayin al’umma.

Wani lokaci a kan samu wasu mata suna gaya wa mazajensu “Me ka taba yi mini” wato duk alherinsa maimakon godiya sai su kushe. Haka nan wasu matan idan suna magana da mazajensu kamar suna magana da wani azzalumi babu wata kalma ko magana mai dadi. Haka nan ta bangaren mazaje akwai irin wadannan mutane masu jahiltar rayuwa da manufa da hadafin yin aurensu.

Harshe ya fi komai hadari, saudayawa masu kin kasashen musulmi da masu ganin hada husuma tsakanin musulmi da ‘yan’uwansu na zaman kasa daya sukan yi amfani da harshe da yada jita-jita don ganin sun kawo husuma da yaki. Kuma saudayawa irin wannan ya faru a kasashenmu da biranenmu kuma ya jawo kashe dubunnan mutane! mu sani babu wani abu da ya fi harshe santsi da hadari don haka sai a kiyaye shi.

Hakkin Kiyaye Jinmu

Ya wajaba a kiyaye ji daga sauraron haram da jita-jita musamman ga mai maganar da an san ba ta da tushe, da yawa mutanen da aka saurare su maganarsu ta zama bala’i ga al’umma da kuma ga mai sauraron. Haka nan ana son sauraron magana mai amfani kamar ta Ilimi da sauraron karatun Kur’ani (musamman ga mai ciki), kuma mai magana da kai yana da hakkin ka saurare shi idan ya gama maganarsa sai ka yi taka.

Hakkin Kiyaye Ganinmu

Ya wajaba a kiyaye gani daga haram[62] musamman kallon namiji ga mace, Musulunci ya hana kallo mai tayar da sha’awa ko kuma da nufin tayar da sha’awa, kamar yadda ya hana kallon jikin mace ajnabiyya in banda fuska da tafuka koda ba tare da nufin sha’awa ba. Haka nan yana hana mace kallon abin da maza bisa al’ada sukan rufe shi na daga jikinsu, amma in ba haka ba, ba ya zama haramun. Amma idan ya zama a matsayi na dole kamar a matsayi na magani da ba wani mai iyawa sai ajnabi to a bisa lalura ya halatta idan zai yiwu ta madubi ko ruwa, idan ba zai yiwu ba to a lokacin yana halatta da idanu[63].

Haka nan akwai abubuwan da ya halatta da wanda bai halatta ba a gani a telebijin da satalayet da bidiyo da hoto kamar tsaraici. Haka nan yana da kyau ga iyaye su kayyade wa yara lokacin kallonsu domin yakan hana su karatu, a wannan kwanaki an samu lissafi mai yawa a kasashen Yammacin duniya na kallon telebijin da ya sanya karatun yara ya yi rauni sosai.

Hakkin Yin Aiki Ga Dukkan Musulmi

1-Shari’ar Musulunci tana daukar yin aiki don samun biyan bukatun rayuwa ga mutum ko ga wanda daukar dawainiyarsa ta zama dole a kansa a matsayin wajibi, kuma ta wajabta wa wanda ake bi bashi kuma yake da ikon yin aiki da ya yi aiki don biyan bashin da yake kansa.

2-Haka nan Shari’ar Musulunci tana daukar yin aiki don yalwatawa cikin ciyarwa, samar da jin dadin rayuwa, da ayyukan alheri, a matsayin mustahabbi da take kwadaitar da mutum a kan yin su.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next