Hakkoki A Musulunci



Yayin nan sai Imam (A.S) ya ambaci hakkoki bakwai, bayan ya fada game da na farkonsu cewa: “Mafi saukin hakki daga cikinsu shi ne ka so wa dan’uwanka kamar yadda kake so wa kanka, ka kuma ki masa abin da kake ki wa kanka”.

SubhanalLahi! Wannan shi ne hakki mai kankanta, to yaya wannan hakkin mafi kankanta yake a garemu yau mu musulmi? Kaicon fuskokin da suke da’awar musulunci amma ba sa aiki da mafi kankantar abin da ya wajaba na daga hakkokinsa. Abu mafi ban mamaki kuma shi ne, a dangata wannan rashin ci gaban da ya samu musulmi ga musulunci, alhalin laifi ba na kowa ba ne sai na wadanda suke kiran kansu musulmi amma ba sa yin aiki da mafi karancin abin da ya wajabta musu da su yi aiki da shi na koyarwar addininsu.

Domin tarihi kawai, kuma don mu san kawukanmu da takaitawarta zamu ambaci wadannan hakkoki bakwai wadanda Imam (A.S) ya bayyana su:

l- Ka so wa dan’uwanka musulmi abin da kake so wa kanka, kuma ka ki masa abin da kake ki wa kanka.

2- Ka nisanci fushinsa, ka bi yardarsa, kuma ka bi umarninsa.

3- Ka taimake shi da kanka, da dukiyarka, da harshenka, da hannunka, da kafarka.

4- Ka zamanto idonsa, dan jagoransa, kuma madubinsa.

5- Kada ka koshi, shi kuma yana cikin yunwace, kada ka kashe kishirwarka shi kuma yana jin kishirwa, kada ka zama a suturce shi yana tsirara.

6- In kana da mai hidima shi kuma dan’uwanka ba shi da mai hidima, to wajibi ne ka tura mai hidimarka, sai ya wanke masa kaya, ya dafa masa abinci, ya gyara masa shimfida.

7- Ka kubutar da rantsuwarsa, ka amsa kiransa, ka gaishe da maras lafiyarsa, kuma ka halarci jana’izarsa. Idan kuwa ka san yana da wata bukata sai ka yi gaggawar biya masa ita, kada ka bari har sai ya tambaye ka, sai dai ka gaggauta masa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next