Hakkoki A Musulunci3- Umarnin iyaye ana gabartar da shi a kan wajibi kifa’i[46]. 4- Kada a daga sauti kan sautin iyaye ko gabata gaba gare su[47]. Hakkokin ‘Ya’ya A Kan Iyaye
Daga nasihohi tattararru da suke cikin wasu hadisai su ne; Kada ka fusata danka ba tare da hakkin shari’a ba, wannan yana iya sanya masa jin haushi, da son barna, da daukar fansa, da nisantar gida ta hanyar kusantar mutanen banza. Haka nan an yi wa uba da yake tura dansa cikin biyayyar iyaye saboda kyawawan dabi’unsa rahama [48]. Game da tausasawa cikin mu’amala wannan ya zo cewa, sauki shi ne yake kawata komai[49], tsanantawa ita ce take bata komai, haka nan mata da ‘ya’ya ana son a biyar da su daidai yadda zasu iya da gwargwadon karfinsu, kuma a yarda da dan kadan da zasu iya ba kausasawa ko tsanantawa. Game da girmama ‘ya’ya a mu’amala ya zo cewa; Manzon Rahama (S.A.W) idan Fadima (A.S) ta shigo Gidan yakan tashi daga wajansa, ya kama hannunta, ya sumbance ta, ya zaunar da ita kan shimfidarsa[50]. A daidaita tsakanin ‘ya’ya hatta a kallo: Da uba zai rika yi wa wannan kallon wulakanci ba dalili, amma wancan kuma ana lallashinsa to ba abin da wannan zai haifar sai kaiwa ga tarwatsawa da rarraba tsakanin ‘ya’yan[51]. Annabi Ya’akub (A.S) ya kasance a aikace ba ya rabawa tsakanin ‘ya’yansa, ba ya fifita wani a kan wani a aiki da mu’amala, amma ya kasance yana nuna wa Yusuf (A.S) soyayya domin Allah ya zabe shi, Sannan shi ne salihi a cikinsu da shi da dan’uwansa, kuma shi ne karami yana da hakkin soyayya da akan nuna wa yara. Amma da yake ‘yanuwansa mujrimai ne sai wannan ya sanya haushi ya rike su suka nemi kashe Annabin Allah su huta saboda soyayyar da yake da ita ta musamman wajan Annabin Allah Ya’akub (A.S), Sannan suka zo suka yi karya da kyarkeci don cimma mugun kaidinsu. Wannan mun kawo shi ne domin kare Annabi Ya’akub (A.S) da barrantar da shi daga zunubi ko laifi da wasu suke jinginawa gareshi. Kyautata sunan ‘ya’ya da sanya musu sunan Annabawa da wasiyyansu; kamar Muhammad da Ibrahim da Ali, ko kuma sunan da aka danganta zuwa ga Allah kamar Abdullahi da AbdurRahman, ko sunan salihan bayi kamar Fadima da Maryam da Khadija ko Lukman. Haka nan tarbiyyar ‘ya’ya tana daga wajibi na farko a kan iyaye kamar yadda ya zo a Hadisai. Hakkokin Dan’uwa A Kan Dan’uwansa
Da farko muna iya cewa musulmi duka ‘yan’uwan musulmi ne saboda haka hakkin da yake hawa kan dan’uwa yana hawa tsakaninsu amma dan’uwa na jini yana da kari kan dan’uwa na musulunci da kamar wajabcin sadar da zumuncinsa. Daga cikin hakkokin dan’uwa a kan dan’uwansa su ne: Yi masa nasiha da kare shi daga wahalhalun da zaka iya taimaka masa wajan maganinsu kamar taimakonsa wajan sana’a, da samun magani, da kudin makaranta, da biyan bukatunsa, da kokarin kawar masa da talauci, da taimakonsa a kan makiyinsa. Malam Muzaffar a Littafinsa yana cewa: Daga cikin mafi girma da kyawun abin da Musulunci ya yi kira zuwa gareshi shi ne ‘yan’uwantaka tsakanin musulmi a kan duk sassabawarsu da martabobinsu da mukamansu. Kamar yadda mafi munin abin da musulmi suka yi a yau da kuma kafin yau shi ne, sakacinsu wajan riko da wannan ‘yan’uwantaka ta musulunci. Domin mafi karancin koyarwar wannan ‘yanuwatakar ita ce “Ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, kuma ya ki masa abin da yake ki wa kansa, kamar yadda zai zo a hadisin Imam Sadik (A.S). Ka duba ka yi tunani a kan wannan dabi’a mai sauki a mahangar Ahlul Baiti (A.S), za ka samu cewa yana daga mafi wahalar abin da zaka iya samu wajan musulmi, da musulmi zasu yi wa kansu adalci su san addininsu sani na hakika, su yi riko da wannan dabi’a ta so wa dayansu dan’uwansa abin da yake so wa kansa, da ba a ga zalunci daga wani ba ko ketare iyaka, ko sata, ko karya, ko yi da wani, ko annamimanci, ko zargi da mummuna, ko suka da karya, ko wulakanci, ko girman kai. Idan da musulmi sun tsaya sun fahimci mafi karancin ma’anar hakkin ‘yan’uwantaka a tsakaninsu kuma suka yi aiki da ita, da zalunci da ketare iyaka sun kau daga bayan kasa, kuma da ka ga ‘yan Adam sun zama ‘yan’uwa suna masu haduwa da juna cikin farin ciki, kuma da mafi daukakar sa’adar zamantakewa ta cika garesu, kuma da mafarkin malaman falsafa na da na samar da mafificiyar hukuma ya tabbata, da sun kasance masu musayar soyayya a tsakaninsu, da ba su bukaci wasu hukumomi da kotuna ba, ko ‘yan sanda, ko kurkuku, ko dokokin laifuffuka, da dokokin haddi da kisasi ba, kuma da ba su rusuna wa ‘yan mulkin mallaka ba, kuma da dawagitai ba su bautar da su ba, kuma da kasa ta canja ta zama aljannar ni’ima kuma gidan sa’ada.
|