Mace a Inuwar Musulunci



Sannan kuma yana magana game da matar Fir'auna Asiya, da Maryam mahaifiyar Annabi Isa (a.s.), yana bijiro da su a matsayin mata madaukaka abin koyi ga zamunan dan Adam, inda ya ce:-­

"Allah Ya buga misali ga wadanda suka ba da gaskiya (na) matar Fir'auna, lokacin da ta ce: `Ya Ubangiji Ka gina min gida a wurinKa a Aljanna, kuma Ka tserar da ni daga Fir'auna da aikinsa, kuma Ka tserar da ni daga mutane azzalumai. (Wani misalin) kuma da Maryamu `yar Imrana wadda ta kiyaye farjinta, sai Muka yi busa a cikinsa daga RuhinMu, ta kuma gaskata ayoyin Ubangijinta da IittattafanSa, ta kuma kasance cikin masu bautar Allah". Surar Tahrim, 66:11-12.

Mu karanta wadannan ayoyi biyu kuma lura da abubuwan da suka kunsa na tunane-tunane masu kyau wadanda ke magana a kan matsayin mace da girmamawa da mutuntawa, babu wata wayewa da abin duniya na zahiri

da ta ba ta irin shi. Hakika AlKur'ani, a aikace, ya gabatar da managarciyar mace a kan maza da mata, ya kuma bukace su da yin koyi da ita cikin fadarsa:

"Allah Ya buga misali ga wadanda suka ba da gaskiya" Surar Tahrim, 66:11. domin kalmar: "Allah Ya buga misali" da "ga wadanda suka ba da gaskiya...", kamar yadda yake bayyane, suna nuna wata wayewa ta imani makadaiciya a duniyar tunani, da wata wayewa da ta kebanta ga managarciyar mace; hakika an sanya ta babbar abar koyi ga maza kamar yadda take abin koyi ga mata cikin akida da matsayin siyasa; sai ya bijiro da wasu misalai biyu na daukakar mutuntakar mace Mumina da matsayinta a tunanin Musulunci, sai ya bijiro da matar Fir'auna sarauniyar Masar, matar gidan mulki da siyasa da babbar daula a waccan duniyar, wadda ta kalubalanci babbar daula; da Maryamu 'yar Imrana wadda ta kalubalanci manyan Bani Isra'ila da makirce-makircensu da mummunan yakinsu a kanta.

Kamar yadda mace ta kasance tana da gudummawarta a rayuwar Ibrahim, Musa, Isa (a.s.); haka nan za mu same ta tana da bayyananniyar gudummawa mai girma a rayuwar Annabi Muhammadu (s.a.w.a.) da da'awarsa. Hakika wannan zango na akida makadaici ya shaida Khadija bint Khuwalid Bakuraishiya (r.a.), wadda ta kasance mace mai babban matsayi a cikin al'ummar garin Makka, mai dukiya da kasuwanci da ra'ayi. Ta kasance farkon wadda Annabi (s.a.w.a.) ya fara magana da ita da kiranshi -bayan Ali (a.s.)­kuma ta yi imani da shi ta gaskata shi, ta bayar da dukiyarta

masu yawa don taimakon kiran shi, ta fuskanci nau'o'in cutarwa da wahalhalu tare da shi na tsawon shekaru goma daga rayuwarta; ta shiga shigifar nan tare da shi, ta jure wahalhalun takunkumin nan da ya ci gaba har na tsawon shekaru uku, sai ta zama cikin mutane mafi girma a tarihin Musulunci; don haka ne ma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kira shekarar da ta rasu a ciki da shekarar bakin ciki.

Musulmi na matukar girmama wannan mata, kuma suna koyi da halayensa da irin wadancan matsayai na ta masu girma.

A wata muhawara da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi da matarsa A'isha (r.a.), a wani martani da ya mayar ga wata maganarta, ya ce:­

"Wallahi Allah bai sauya min ita da wadda ta fi ta ba, ta kasance uwar iyali, mai tarbiyyar gida, ta yi imani da ni lokacin da mutane suka karyata ni, ta taimaka min da dukiyarta lokacin da mutane suka hana ni, kuma an azurta ni da `ya'ya ta hanyarta aka hana ni da wasunta".l2



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next