Mace a Inuwar MusulunciBabu wata surar hakikanin Musulunci a kwakwalwar mutumin yamma, maimakon haka, duk abin da ke cikin kwakwalwarsa da fahimtarsa ita ce mummunan sura. kuma da mutumin yammaci ya san hakikanin Musulunci da ya yi maraba da shi. kuma da ya bude hankalinsa don yin muhawara ta ilimi. haka da ya karbe shi da `yanci da budaddiyar kwakwalwa. A takaice za mu iya karanta wannan babbar matsala cikin jawabin da shugaban kasar Jamus Roman Hutsog ya yi a ranar 10/1/1995 a lokacin bikin girmama baturiyar nan masaniyar kasashe da al'adun Musulmi (Mustashrika) a kasar Jamus, Anamari Shamel, mai adalci cikin abubuwan da take rubutawa da fada, a lokacin bukin bata kyautar zaman lafiya da kungiyar marubutan kasar Jamus ta ba ta. Ya fadi abin da ya fada ne yana mai mayar da martani ga masu sukan kyautar zaman lafiya da aka ba Shame[ saboda kawai tana kariya ga tunane-tunanen Musulunci, kuma tana mu'amala da shi bisa gaskiya da adalci.tana kuma kira zuwa fahimtarsa da sauya mummunar surar da kafafan watsa labaran Turawa ke yi ga Musulunci da Musulmi; sai ya ce: "Akwai wani al'amari da ke bayyane karara cikin alaka da mu'amalarmu da Musulunci a wannan lokacin da muke ciki. Ba za mu yi karya ga ra'ayin da ya watsu a Jamus ba, idan muka ce: abin da ke zuwa cikin tunanin mafi yawanmu a duk lokacin da aka ambaci Musulunci shi ne: `Dokokin uKuba na rashin tausayi' ko `rashin sassaucin addini' ko zaluntar mace ko tsaurin ra'ayi irin na adawa. sai dai wannan Kuntata yanayi ne da ya wajaba mu sauya shi; mu tuna da ambaliyar nan ta hasken Musulunci wadda tun kafin Karnoni shida ko bakwai ta kiyaye wa kasashen yammaci wani sashe babba na tsofaffin abubuwan tarihi, wadda kuma a wancan lokacin ta sami kanta a gaban wani irin nau'i na tunanin yammaci; babbu shakka (wannan ambaliya) ta ji cewa ashi (wannan nau'i na tunanin yammaci) mai tsaurin ra'ayi ne mara sassauci". A yankin karshe na maganarsa, shugaban na Jamus ya yi bayanin dalilin adawa da Musulunci da cewa shi ne jahiltar da Turawa suka yi wa Musulunci, kan haka za mu same shi yana cewa: "Ashe ba ta yiyuwa dalilin rashin fahimtarmu ga Musulunci ya zamashi ne ginuwarsa a kan asasai masu zurfi na al'umma mai riKo da addini alhali mu masu riko ne ta fuska mai girma da wani tafarki da bai yarda da addini ba? dan haka ya tabbata ya ya za mu yi mu'amala da wannan nazari mai matsala? Shin ya yi daidai mu siffanta Musulmi masu tsoron Allah da siffofin `masu tsattsauran ra'ayi, 'yan ta'adda' don kawai mu mun rasa ingantaccen riskar yadda izgili yake a zukatan mabiya wasu addinai, ko kuwa saboda mun zama ba za mu iya bayyana irin wannan ingantacciyar fahimta ba?". Daga nan sai shugaban na Jamus ya bayyana cewa shi bai san Musulunci yadda ya kamata ba sai bayan da ya karanta littaffan wannan Mustashrika mai adalci (wato Shamel), sai ya ce: "Tsinkayata ga irin wannan babban nau'i na fuskance-fuskance cikin tarihin Musulunci da hakikaninsa a halin yanzu bai fara ba sai ta hanyar littafan Anamari Shamel, akwai kyakkyawan zaton kuma cewa wasuna ma sun fuskanci irin wannan gwaji. Hakika muna bukatar musanya abin da ya kuke mana na fahimtar sashinmu ga sashi... ". Sannan sai shugaban na Jamus ya yi kira da a fahimci Musulunci don shata wani matsayi game da shi koma bayan matsayin da ya ginu a kan jahiltar sa, sai ya ce: "Ina yin ikirari da cewa a gabanmu babu wani zabi face kara samun masaniya game da duniyar Musulmi matukar muna nufin yin aiki don kare hakkin dan Adam da Dimokuradiyya". Sai kuma ya kara da cewa: "Hakika babban dalilin son sanin Musulunci da fahimtar wadatacciyar wayewar nan ta shi ya samo asali ne daga kasancewarmu cikin wata wayewa da ba shi ba. Hakika kuwa uwargida Shamel ta fadaka da wannan bukata ta rai, ina fata kuma wannan ya zama shi ne yadda wasuna masu yawa ke ji..". "Hakika Uwargida Anamari Shamel ta share mana fagen haduwa da Musulunci.. 11 Hakika wannan rikici na bayar da kyautar zaman lafiya a kasar Jamus ga masaniyar kasashe da al'adun Musulmi (Shamel) a shekara ta 1995, da dacewan `yan siyasa da wayayyu daga ma'abuta tunani, shehunnan malamai, Turawa masana kasashen Musulmi da al’adun Musulunci, ma'abuta fanni da adabi a kasar Jamus, wadda ake dauka daga cikin manyan daulolin duniya a tarihin wannan zamani namu, da nasarar bangaren Shamel, wato masu kira zuwa a fahimci Musulunci a bisa hakikaninsa don shata matsaya, daga cikin wadanda ke sahun gaba na wadannan kuwa har da manazarta da 'yan siyasa, a cikin su har da shugaban kasar Jamus wanda muka karanta muhimman zantuttukansa; duk yana nuna mana wani abu ne mai girma daga abubuwan da ke wuyan Musulmi marubuci, manazarci kuma ma'abucin fanni da adabi. kamar yadda ya ke wuyan cibiyoyi da malaman addini. wannan kuwa shi ne nauyin yin bayanin Musulunci a bisa hakikaninsa mai haske. wanda yake tafiya tare da hankali da zuciya cikin sauki. ta hanyar aiki da tafarkin nan na AIkur'ani wajen kira zuwa ga Allah Madaukaki: "Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau, kuma ka yi muhawara da su kan abin da yake shi ya fi kyau.." Surar Nahali, 16:125.
|