Mace a Inuwar MusulunciAmma lokacin da rayuwar aure ta cika da matsaloli da damuwa da tashe-tashen hankula, to wannan yana tasiri mara kyau ga miji, aikinsa, neman abinci da alakokinsa da wasu. Kamar yadda yanayoyin rai a cikin iyali ke tasiri ga miji, haka yake tasiri ga `ya'ya; domin yaron da ya tashi cikin yanayin kiyayya, rikice-rikce, matsaloli da mummunan mu'amala, da wuya ya zama daidaitaccen mutum cikin halayyarsa da alakokinsa da wasu, da fuskantar da iyawarsa ta tunani da jiki; domin so tari yaro, saboda yanayin mummunar tarbiyya, yakan sauya ya zama karkataccen mutum mai adawa, ko malalaci da ba ya amfanin komai, ko birkitacce mai kawo matsaloli da aikata laifuka. Alhali kyakkyawar tarbiyya na taimakawa wajen samar da mikakken mutum, ta yadda irin wannan tarbiyya ke tasiri a rayuwar gobe ta yaro ta ilimi, zamantakewa da tattalin arziki. Don haka gudummawar mace ke da tasiri wajen ginin zamantakewa ta hanyar tarbiyya da tanajin ingantattun mutane ga al'umma; haka nan ta hanyar samar da yanayi mai kayu ga miji. A cikin wadannan nassosi Akur'ani mai girma da hadisai masu tsarki sun iyakance asasai da ka'idoji na dokokin, halayya, tarbiyya, tsari da gudanar da iyali; a kan wannan hanya kuma mace na taimakawa wajen ginin al'umma. Ginin al'umma kuwa ya ginu a kan asasai kamar.Soyayya da kauna da jin kai da girmamawa tsakanin ma'aurata. b-Mace na da hakkoki kamar yadda wajibobi suka hau kanta. c-Maza ke rike da nauyin shugabanci da daukar dawainiyar gudanar da al'amurran gida. d-Taimakekeniya cikin sha'anonin rayuwar aure. e-Yin tsaka-tsaki wajen ciyarwa da kiyaye tattalin iyali. f-Kula da nauyi, wato kulawar miji da nauyin da ya hau kansa game da matarsa da sauran wadanda ke cikin iyali; da kulawar mata da nauyin da ya hau kanta game da mijinta, `ya'yanta da iyalin ta. Domin a kanta nauyin kulawa da gida da `ya'ya, tarayya wajen ba su ingantacciyar tarbiyya da yin mu'amala da su da kauna da tausayi da kulawa. Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria.
|