Mace a Inuwar Musulunci



Surar A'arafi, 7:189.

"Maza sama suke da mata saboda abin da Allah Ya fifita sashensu (da shi) a kan sashi, da kuma abin da suke ciyarwa daga dukiyoyinsu. Sannan mata na gari masu biyayya ne (kuma) masu kiyaye asirin abin da ke boye wanda Allah Ya kiyaye..." Surar Nisa'i, 4:34.

"..kuma suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu ke da hakkoki) a kansu da kyautatawa.." Surar Bakara, 2:228. "..Kuma ku zauna da su da kyautatawa.."

Surar Nisa'i, 4:19.

"Kuma ma'abucin yalwa ya ciyar daga yalwarsa.." Surar Dalaki, 65:7. "Kuma ku taimaki juna da aikin alheri da tsoron Allah, kuma kar ku taimaki juna a kan yin sabo da ta'adda.." Surar Ma'ida, 5:2.

Haka nan kamar yadda AIkur'ani mai girma ya yimagana game da asasai da alakokin `yan Adamtaka da doka a iyali, haka nan ma hadisan Annabi suka yi magana a kan haka, za mu ambaci abin da aka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.):­

"Dukkan ku masu kiwo ne kuma wadanda za a tambaya a kan kiwonsu; sarki da ke saman mutane mai kiwo ne kuma abin tambaya a kan abin da yake kiwo, namiji mai kiwo ne a kan iyalinsa kuma shi abin tambaya ne a kansu; mace mai kiwo ce a kan gidan mijinta da `ya'yanshi kuma ita abar tambaya ce a kansu, bawa mai kiwo ne a kan dukiyar ubangidansa kuma shi abin tambaya ne a kan shi. Ku saurara, dukkan ku masu kiwo ne, kuma kowannenku abin tambaya ne a kan abin da yake kiwo."16

Da abin da aka ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) cewa:­"Daga cikin dabi'un Annabawa akwai son mata".

Da abin da aka ruwaito daga gare shi (a.s.) cewa:­"Bana tsammanin mutum na kara alheri a kan imani har sai ya kara so ga mata.J7

Yana da kyau a nan mu yi ishara da cewa ginin da mace ke yi a cikin al'umma a wasu lokuta ya kan zama aiki ne kai tsaye, a wasu kuma ya kan zama ta hanyar alakarta ta rai da halayya da miji da `ya'ya. Matar da ke samar da yanayin hutawa da kyakkyawan zamantakewa da miji, take kuma tabbatar da kauna, soyayya da kwanciyar hankali, kamar yadda ya kamata a alakokin da ke tsakaninsu, to irin wadannan yanayoyi na rai suna tasiri ga miji da alakarsa ta zamantakewa da wasu, da ikonsa na neman abinci da bayarwa. wannan kuwa saboda yanayin rai ga mutum yana tasiri a daukacin harkokinsa da alakokinsa da wasu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next