Tattaunawa Ta Bakwai



 Ka nemi ci gaba da bahasin nan amma ina ganin kowa ya yi tasa fahimtar ya fi kyau, sa'an nan mu kaunaci juna kan abin da muka hadu, mu girmama juna kan abin da muka rabu.

Amma da kake son sanin matsayin wadanda suka ki biyayya ga Ali (a.s) sai na ce maka: Hukuncin wurin Allah koda kuwa wani ya yi hasashe yana iya zama kuskure domin wannan wani abu ne da yake a hannun Allah kawai.

Amma musulmin duniya kowa yana da nasa ra'ayi a kan hakan, domin akwai wanda ya hana a ma koma baya a kalli wannan kuskure da ya faru da ya hada da barin wasiyyar Annabi (s.a.w) kan wanda zai gaje shi a tafiyar da lamurran al'umma bayansa, don haka ne ma wasu suka yi kokarin toshe wannan kuren da cewa; ba a ma yi wasiyya ba duk da lamarin wasiyya da Littafin Allah da Alayen Annabi (s.a.w) wani abu ne mutawatiri. Sa'an nan ga lamarin kwacewa 'yar manzon Allah gonarta da manzon Allah ya ba ta wacce aka fi sani da Fadak wadda hatta da asbabun nuzul na Suyudi da littattafai da yawa sun yi magana kan yadda manzon Allah ya ba ta Fadak, da yi mata bulala, da kuma mafi muni shi ne dukanta da yin sanadin barin cikin danta Muhsin da kuma fasa kyauren gidanta da ya jawo huda kirjinta da fasa shi da kusoshi biyu wanda ya yi sanadin rayuwarta har ta yi fushi da al'ummar musulmi gaba daya ta nemi a boye kabarinta kada kowa ya sani domin kawai ta nuna fushinta da wannan al'umma, har ma Buhari ya kawo maganganunta masu zafi kan halifofin farko da suka gabaci mijinta Imam Ali (a.s) saboda sha'anin da ya faru na jagorancin al'umma bayan Annabi (s.a.w). Wannan ne ma ya sanya aka samu kowa yana kallon abin ta mahangarsa da da ra'ayoyi iri-iri daban-daban daidai gwargwadon fahimtar kowannensu.

Sai aka kasu gidaje mabanbanta, kowa yana da nasa ra'ayi, sai masu bin koyarwar Banu Umayya da malamansu suka tafi a kan farin ciki da wannan lamari, wani abin mamaki shi ne yin biki da ranar da aka kashe danta wato; Imam Husain (a.s), kwanan nan ne wasu littattafai suke dada karfafa jin dadin abin da ya faru na kashe shi suna masu nuni da gwara haka! kai suna cewa ma laifinsa ne!! wal'iyazu bil-Lah!.

Lamarin sanin matsayin wadanda suka yi watsi da wasiyyar Annabi (s.a.w) lallai lamari ne mai wuyar sha'ani da ya sanya gaba mai tsanani tsakanin musulmi, har ma na kai ga natijar cewa duk wanda ya yi bincike ya samu abin da yake ganin shi ne zai zame masa uzuri har ga Allah to sai ya yi aiki da wannan ya kyale sauran masu ra'ayoyi kowa ya je da nasa in ya so ranar lahira sai Allah ya yi wa kowa hisabi da abin da yake gani maslaha ga kowane bawa daidai yadda ya yi ikhlasi ya cimma gaskiya ba son zuciyarsa a ciki.

Mafi yawancin masu bayani sun kawo wannan canjin a matsayin abin da ya haifar da musibu sakamakon kauce wa Ahlul Baiti (a.s) da ya sanya komai ya jirkice kuma sun fassara wannan lamarin yana cikin irin matsayoyi da Annabi ya yi nuni da shi mai tsanani kan sahabbansa a hadisan nan da Buhari da Muslim da Ahmad da sauran manyan malaman hadisi suka ruwaito kamar haka: Muslim: 4/1793. Buhari: 28/26. Masnad Ahmad: 1/ 253, 258.

A cikin akwai hadisan da suka yi nuni da za a yi wuta da sahabbai sai ka duba, har ma manzon Allah ya ki yarda sai a ce masa ba ka san abin da suka yi bayanka ba. A wasu ruwayoyin sun yi ridda bayanka. Sannan Abuddarda' da Anas dan Malik sun yi furuci tun a zamaninsu da babu wani abu da ake yi lokacin manzon Allah (s.a.w) sai da aka canja shi!

 Hada da abin da manzon Allah (s.a.w) ya gaya wa halifa na farko kamar yadda ya zo a cikin littafin nan na Muwadda'r Malik cewa; Ba zai nema masa gafara ba domin bai san abin da zasu yi ba a bayansa. Kuma wannan lamari na matakin da Annabi ya fada a hadisai madaukaka su ne abin da wasu manyan sahabbai masu daraja kamar su Salman Farisi da Ammar da Bilal suke a kai; sai dai ni bayan bincike da ya dade tare da malamaina na tafi a kan cewa; Wannan lamari ne mai wuyar sha'ani kuma ina ganin wadanda suka yi hakan na saba wa wasiyyar Annabi (s.a.w) da hayewa karagar jagoranci: sun yi ijitihadi ne suka yi kuskure, ba kamar yadda wasu suke ganin sun yi haka ne da gangan domin kwadayin mulki ko kuma neman rusa musulunci. Abu guda ne ba zamu iya korewa ba shi ne akwai kuskure a kan abin da ya faru.

Amma matsayin wadanda basu koyi (takalidanci) da maganganun Ahlul Baiti?: Wannan ma matsayinsu yana koma wa ga Allah madaukaki ne, kuma shi ne zai saka wa kowa da abin da ya yi daidai gwargwadon ikhlasinsa da tsarkin niyya. Domin haka ne kowa sai ya yi sa'ayi "Inna sa'ayakum lashatta.. da ayoyin da suka biyo bayanta.

Sai kowa ya koma ya yi binciken wasiyyar Annabi (s.a.w) da cewa me ya yi wa al'umma wasici da shi, kuma shin al'umma ta kiyaye ko kuwa? Waye ya ce a yi biyayya gareshi bayansa domin ya binciki me ya ce domin ya samu uzurin yin addini daidai a wurin Allah madaukaki? da sauran tambayoyi masu yawa da suke cikin kwakwalenmu.



1 2 3 4 5 6 7 8 next