Imamanci



Imamanci sai da nassi

Mun yi imani cewa lmamanci tamkar Annabci ne ba ya kasancewa sai da nassi daga Allah ta'ala a harshen Manzonsa ko kuma a bisa harshen lmamin da ya kasance da nassi idan har ya so ya ba da nassi game da lmamin bayansa.

Hukuncin lmamanci a kan haka tamkar hukuncin Annabci ne ba tare da wani banbanci ba, mutane ba su da ikon wani hukunci a kan wanda Allah Ya ayyana shi mai shiryarwa da datarwa ga bil Adama baki daya kamar kuma yadda ba su da hakkin ayyana shi ko kuma kaddamar da shi ko zabensa, domin wanda yake da tsarki da kwazon daukar alkyabbar lmamanci baki daya da kuma shiryawa da illahirin bil Adama gaba daya bai dace ya san wani abu ba face da sanarwar Allah kuma bai kamata a ayyana shi ba face da ayyanawar Allah.

Mun yi imani cewa Annabi (S.A.W) Ya ba da nassi game da halifansa kuma lmamin talikai Aliyu Bin Abi Talib Amirul muminina (A.S) amini a kan wahayi lmamin halittu, ya ayyana shi a gurare da dama kuma ya nada shi ya kuma karba masa bai'a a kan shugabancin Muminai ranar Gadir Ya ce: "A ji a fadaka duk wanda na kasance shugabansa ne to ga Aliyu shi ma shugabansa ne, Ya Allah ka so wanda ya so shi ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake shi ka tozarta wanda ya tozarta shi kuma Ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya."Daga cikin guraren farko dangane da nassi a kan lmamancinsa maganarsa(Manzo)yayin da ya kirayi danginsa makusata da 'Yanuwansa na kusa kuma Ya ce :"Wannan shi ne dan'uwana kuma wasiyyina kuma halifana ku bi shi"  a yayin nan kuma shi yana yaro bai balaga ba.Kuma Ya maimaita maganarsa sau da dama cewa: "Kai a gare ni matsayin Haruna ga Musa kake sai dai kawai babu Annabi ne bayana."Da sauran ruwayoyi da ayoyi masu girma da suke nuni da tabbatar shugabanci na gaba daya gare shi kamar ayar da ke cewa: "'Tabbatacce kawai shi ne cewa Allah ne majibincinku da Manzonsa da Wadanda suka yi imani wadanda suke ba da zakka su suna masu ruku'i." Surar Ma'ida: 55.        wannan ta sauka ne game da shi yayin da ya ba sadakar zobensa yana cikin ruku"u.

 Bin diddigin dukan abinda ya zo na daga ruwayoyi da ayoyin Alkur'ani ba ya goyon bayan cewa wannan sakon kagagge ne.kazalika bayani manufofinsu da suke nuni da su. Sa'an nan shi kuma kansa (A.S) Ya ba da nassi game da Imamancin Hasan da Husain (AS), shi kuma Husain ya ba da nassin Imamancin dansa Aliyu Zainul Abidin (AS) haka nan dai Imami ke ba nassin Imami bayan Imami, wanda ya gabata ya ba da na mai zuwa har zuwa kan na karshensu kuma shi ne zababbensu kamar yadda zai zo.

Adadin Imamai

Mun yi imani da cewa Imamai wadanda suke da siffar Imamancin gaskiya su ne wadanda muke komawa gare su a hukunce-hukuncen shari'a wadanda aka ba da nassi game da Imamancinsu su goma sha biyu ne, Annabi (SAW) ya ba da nassi a kansu dukkaninsu da sunayansu, sa'an nan kuma duk wanda ya gabata daga cikinsu to ya ba da nassi a kan wanda ke biye da shi kamar haka:­

Adadi

AI- kunya

Suna



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next