Imamanci



Mun yi imani da cewa Imamai su ne "Ulul-Amri" Shugabannin da Allah ta'ala ya yi umarni a yi musu biyayya, kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane,kuma su ne kofofin Allah kuma tafarkin isa gare shi, kuma masu shiryarwa zuwa gare shi. Kuma su ne taskar ilminsa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma'ajiyar saninSa, don haka su ke aminai ga mazauna bayan kasa kamar kuma yadda suke sune taurarin amincin mazauna sama kamar yadda manzon allah  (saw)ya  fassara kazalika kamar yadda ya fada (saw):lalle misalansu a wannan al’umma kamar jirgin Nuhu(AS) ne wanda ya hau shi ya tsira wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka kamar yadda ya zo Alkur’ani mai girma su “saidai bayi ne ababan girmamawa ba sa zarce shi da magana kuma su da umarnninsa masu aiki ne  surar anbiya: 26-27. 

Kuma su ne wadanda Allah ya tafiyar masu da datti ya tsarkake su sosai, bil hasali ma mun yi imani da cewa umarninsu  umarninAllah Ta'ala ne, biyayya gare su biyayya ce gare shi, saba musu kuma saba Masa ne, kuma Soyayya gare su soyayya ce gare shi, kiyayya gare su kiyayya ce gare Shi, bai halatta ba a mayar musu domin mai mayarwa gare su tamkar mai mayayarwa ga Allah ne.

 Don haka Ya wajaba mika wuya gare su da biyayya ga umarninsu da riko da maganganunsu, Saboda haka Mu mun yi imani cewa hukunce-hukuncen Shari'ar Ubangiji ba sa samun shayarwa sai dai daga ruwansu, kuma bai halatta a karbe ta sai dai daga gurinsu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba Ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu. Kuma mukallafi ba Ya samun kwanciyar hankalin cewa Ya ba da wajibin da aka dora masa face ta hanyarsu, Su kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S.) suke duk wanda ya hau to Ya tsira wanda kuwa ya jinkirta ya bar su to Ya dulmuye a cikin wannan ambaliyar da ke makare da igiyoyin ruwan rikitarwa da bata da da'awowi da rikice- rikice.

A wannan zamanin bayanin tabbatar da lmamai (A.S.) a matsayin cewa su ne halifofin gaskiya a shar'ance kuma shugabanni zabin ubangiji domin wannan al'amari ne da ya riga ya shude a tarihi kuma tabbatar da hakan ba zai sake dewo mana da zamanin da ya wuce na tarihi ba, ko kuma ya dawo musu da hakkinsu da aka kwace na tafi da hukuncin Allah na shari'a ba, da kuma samar da abinda Manzon Allah (S.A.W) kamar yadda Ya zo da shi din ba.

Sai dai kuma karban hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kuma Mujtahidan da ba sa sha daga daddadan ruwan mashayarsu to nesanta ne daga tafarkin sawaba a addini, kuma baligi ba ya taba samun kwanciyar hankalin cewa ya saukar da abinda aka kallafa masa daga Allah ta'ala, domin tare da kaddara cewa akwai sabanin ra'ayoyi a tsakanin jama'ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari'a , sabani irin wanda babu mai sa ran yin daidai a kansa to kuwa babu wani abu da ya saura ga mukallafi face ya juya ga mazhabar da ya so da kuma ra'a yin da ya zaba, kai babu makawa gare shi face ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah Ta'ala wajen ayyana mazhaba kebantacciya wadda Ya hakikance cewa da ita ne zai isa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ne zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abinda ake da yakinin wajibcinsa babu makawa yana bukatar a samu yakinin saukar da shi.

Dalili tabbatacce da ke nuna wajabcin komawa ga Ahlul Bait da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce bayan annabi (S.A.W) akalla shi ne maganar manzon Allah(S.A.W) "Ni lalle na bar muku abinda idan har kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada bayana, shi ne abubuwa biyu masu nauyi, dayansu ya fi daya girma, wato littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa da kuma zuriyata mutanen gidana ku ji ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su iske ni a tabki."

Wannan hadisin masu ruwaya a tafarkin Sunna da Shi'a sun yi ittafaki a kansa don haka ka kyautata nazarin wannan hadisin da kyau za ka iske abinda zai gamsar da kai ya kuma ba ka mamaki a ma'anarsa da abinda Ya kunsa, manufar maganar Manzo "Matukar kun yi riko da shi ba kwa taba bacewa bayana bar abada", tana da zurfi, kuma abinda ya bari a tsakaninmu masu nauyi guda biyu ne a hade tare, domin ya sanya su ne kamar abu guda daya bai wadatu da a yi riko da guda daya ba kawai daga cikinsu. saboda haka ta riko da su tare ne kawai ba za mu taba bacewa ba bar abada.

Kuma ma'anar fadinsa (S.A.W) cewa "Ba za su taba rabuwa ba har su iso gare ni a tabki" a sarari take sosai, wato wanda ya raba tsakaninsu bai yi riko da su tare  ba to ba ya taba samun shiriya har abada, wannan kuma shi ne abinda ya sa suka zamanto '`Jirgin ruwan tsira" da "Amincin Allah a bayan kasa". Kuma duk wanda ya jinkirta ya dakata ya bar sa to ya nutse a cikin guguwar bata ba kuma zai amintu daga halaka ba, fassarar wannan kuwa da soyayya gare su ne kawai ba tare da riko da maganganunsu da bin hanyarsu ba guje wa gaskiya ne, babu abinda ke kaiwa ga hakki illa ra'ayin rikau da gafala daga ingantacciyar hanya a bisa fassarar bayyanannen zancen Larabci 

Son Ahlul Bait (A.S.)

Allah Ta'ala Yana cewa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next