Imamanci



"Kuma babu wata al'umma face mai gargadi Ya zamanto a cikinta." Surar Fatir: 24.

Ismar Imami

Mun yi Imani da cewa Imami ma tamkar Annabi wajibi ne Ya zama katangagge daga duka munanan ayyuka da alfasha, na zahiri da na badini, daga yarinta har zuwa mutuwa, da mantuwa ko da ganganci, Kazalika wajibi ne Ya zama katangagge daga kuskure da mantuwa da rafkanuwa domin Imamai masu kare shari'a, masu tsayiwa a kanta, halinsu tamka halin Annabi ne. Dalilin kuwa da ya hukunta mana imam da ismar Annabawa haka na shi ne dalilin da ya hukunta mana imani da ismar Imami ba tare da wani bambanci ba, kuma ba gagararre ba ne ga Allah(SWT) Ya tare talikai duk cikin abu daya duk jimillah

Siffofin Imami

Mun yi imani cewa imami tamkar Annabi shi ma ya wajaba ya zamanto mafificin mutane a siffofin kamala, kamarsu jaruntaka, da karimci, da kame kai, da gaskiya, da adalci, da tafi da al'amura, da hikima da kuma kyawun hali, dalilinmu kuma game da Annabi shi ne ainihin dalilanmu ma game da Imami a game da haka...

Dangane da Iliminsa, kuwa, shi yana samun saninsa da hukunce­ hukuncen ubangiji da dukan masaniyar sa ne ta gurin Annabi ko kuma Imamin da ya gabace shi, Idan kuwa aka sami wani sabon abu to babu makawa ya san shi ta hanyar ilhami daga karfin kwanyar da Allah Ya cusa masa, idan ya mai da hankalinsa a kan wani al'amari yana so ya san hakikaninsa to ba ya kuskure kuma ba ya rikirkicewa kuma ba ya bukatar hujjoji na hankali a kan haka kuma ba ya bukatar fahintarwar Malamai koda yake ilimin nasa na iya karuwa ya kara inganta, wannan shi ne abinda ya sa Annabi (S.A.W) a addu'arsa yake cewa: "Ubangiji ka kara mini ilimi." Yana kunsa a fadar Allah "Ka ce Ya Ubangiji Ka karamini ilimi." Surar Taha: 114.

Na ce: Ya tabbata a ilimin sanin halayya cewa kowa yana da wata sa'a ayyananniya ko ma awowi da yakan san wani abu shi da kansa ta hanyar kaifin fahinta wanda shi a kan kansa reshe ne na ilhami, saboda abinda Allah Ya sanya masa na karfin yin haka, wannan kudurar ta sha bamban wajen tsanani da raunana, da karuwa da kuma raguwa a bil Adama gwargwadon sabanin daidaikunsu, sai tunanin mutum ya kai ga sani a wancan lokacin ba tare da bukatar ya tsaya ya yi tunani ko kuma tsara mukaddima da hujjoji ba ko kuma koyawar malamai ba, kuma sau da yawa mutum kan sami irin haka sau da yawa a kan kansa a rayuwa, Idan kuwa al'amarin haka yake to ya halatta ga mutum Ya kai ga madaukakan darajojin kamala a karfin tunaninsa na sanin ilhami. Wannan kuwa abu ne da masana falsafa nada da na yanzu.

Don haka mike cewa: shi a kan kansa: to lalle karfin ilhami a gurin Imami da ake kira "kuw-wal kudsiyya" Ya kai ga mafi kololuwar darajar kamala, don haka yana da tsarkakar ruhi da ke daidai da karbar sannai a kowane kokaci ta kowane hali, don haka duk lokacin da Ya mai da hankali ga wani abu daga abubuwa yana bukatar Ya san shi sai Ya san shi da wannan kudurar ta "Kuwwa Kudsiya" ta Ilhami ba tare da jinkirtawa ba ko shirya wasu mukaddimomi ko kuma koyo daga bakin malami, haka abinda yake son sanin zai bayyana gare shi kamar yadda abubuwa ke bayyana a tsafta tacce madubi, babu wani dindimi ko rikitarwa game da abinda Ya so sanin.

Wannan kuwa abu ne da yake bayyananne game da tarihim Imamai (A.S.) tamkar Annabi Muhammadu (S.A.W) ba su yi tarbiyya a hannnu kowa ba, ba su koyi karatu a gurin wani malami ba tun daga farkon rayuwarsu har zuwanu shekarun balaga, koda rubutu ba su koya a gurin wani ba, bai tabbata ba cewa daya daga cikinsu Ya shiga gurin koyon rubutu ko Ya yi almajiranci a hannun wani malami a kan wani abu duk kuwa da cewa kuwa suna da matsayin ilimi da ba a iya kintatawa Kuma ba a taba tambayar wani abu ba face sun ba da amsarsa a lokacin da aka tambaya, ba a taba jin kalmar (ban sani ba) daga bakinsu ko kuma jinkirta ba da amsa har sai sun yi nazari ko tunani ko makamancinsu, alhali kuwa ba za ka taba samun wani daga cikin manyan malaman fikihu ba face wadanda ya yi tarbiyya a hannunsu da kuma guraren da ya ciro ruwayoyinsa ko kuma inda ya sami iliminsa daga mashahurai, da kuma cewa ya dakata a kan wasu matsaloli, ko kuma ya yi shakka a kan al 'amura da dama kamar dai yadda al'adar mutum take a kowane guri a kowane zamani.

Biyayya ga Imamai



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next