Sabuban Soyayya



108. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ‘Yan’uwa suna bukatar abubuwa uku tskaninsu, idan suka yi su, to ya yi kyau, idan kuwa ba haka ba to zasu ba wa juna baya, kuma su yi gaba da juna, abubuwan su ne: yi wa juna adalci, tausaya wa juna, da kawar da hassada[69].

3 / 7

Abin Da Yake Wajabta Tsarkakar Soyayya

109. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: uku suna daga abubuwan da suke tsarkake soyayya: Boye (yafe) aibi, da kiyaye sirri, da kuma taimako a cikin tsanani[70].

110. Daga gareshi (S.A.W): Uku suna tsarkake maka son dan’uwanka: ka yi masa sallama idan ka hadu da shi, ka matsa masa a wajen zama, ka kuma kira shi da mafi soyuwar sunaye gunsa[71].

111. Daga gareshi (S.A.W): daga abin da yake kawo maka soyayyar dan’uwanka musulmi ka kasance a bayan idonsa ka fi (amfanarsa) fiye da a gabansa[72].

112. Imam Ali (A.S) ya ce: Soyayya ba ta samuwa ga wanda yake ba mai ladabi ba[73].

113. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: idan kana son ka samu kaunar dan’uwanka gareka, to kada ka yi masa raha, kada ka yi jayayya da shi, kada ka yi masa takama, kada ka nuna shi da hannu[74].

3 / 8

Abubuwa masu kawo soyayya

114. Imam Ali (A.S) ya ce: Hakika yana daga mafi kyawun abin da mutane suke hada zukatansu masoyansu da shi kuma suke kawar da gaba daga zukatan makiyansu da shi, shi ne; kyakkyawan sakin fuska yayin haduwa, da kuma neman juna yayin da ba sa nan, da kuma farin ciki yayin haduwa da su[75].

115. Imam Ali (A.S) ya ce: uku suna kawo soyayya ga juna; kyakkyawan hali, da kyakkyawan tausasawa, da kuma kankan da kai[76].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next