Sabuban Soyayya



c- Kyautata wa zuwa ga mutane

Kur'ani:

“ kuma kyakkyawa ba ta daidaita da mummuna, ka ture da wacce take mafi kyau, sai (ka) ga wanda yake tsakaninka da shi akwai gaba (ya zamanto) kamar masoyi ne majibanci”[44].

Hadisai:

85. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: an dora zukata a kan son wanda ya kyautata mata, da kin wanda ya munana mata[45].

86. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: wanda kyautatawarsa ta yawaita to ‘yan’uwansa zasu so shi[46].

D- Bayar Da Kyauta

87. Annabi Isa (A.S) ya ce: yaya wanda ba ya ba wa masoyinsa wani abu daga abin da yake da shi sonsa gareshi zai cika[47]?!

88. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya bayar da kyauta kafin tambaya shi ne mai karimci abin so[48].

89. Daga littafin Amali na Dusi daga Safwan al’jammal: almu’alla dan khunais ya shiga wurin Abu Abdullah (A.S) yana yi masa ban kwana –yana nufin yin safara- yayin da ya yi masa bankwana sai ya ce: ya mu’alla, ka yi girmamawa don Allah zai girmama ka. Sai ya ce: da me ya dan Manzon Allah (S.A.W)? sai ya ce: ya mu’alla, ka ji tsoron Allah komai sai ya ji tsoronka. Ya mu’alla, ka so ‘yan’uwanka da sadar da zumuncinsu; ka sani hakika Allah ya sanya kyauta soyayya ne, hani kuma kiyayya, kuma ku wallahi idan kuka tambaye ni, na ba ku sai kuka so ni, to ya fiye mini da kada ku tambaye ni ban ba ku ba sai ku ki ni. Ko yaya dai duk abin da Allah mabuwayi madaukaki ya gudanar ta hannuna zuwa gareku to Allah ne abin godewa, kada ku nisanci yin godiya ga Allah sakamakon abin da ya gudanar gareku ta hannuna[49].

E- Nisantar Abin Da Yake Hannun Mutane

­90. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka soyu gun mutane da nisantar abin da yake hannunsu sai ka rabauta da soyayyarsu[50].

F- Aiki Da Gaskiya

91. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya yi aiki da gaskiya sai halittu su karkata zuwa gareshi[51].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next