Sabuban Soyayya



57. Sunan ibn majah daga Abuzar Daga Manzon Allah (S.A.W) na ce masa: mutum yana aiki don Allah sai mutane su so shi a kan haka?! Sai ya ce: wannan shi ne albushir na gaggawa na mumini[16].

4 / 3

Kyawawan Halaye Suna Kawo Kauna

A- Kyakkyawar Niyya

58. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: wanda niyyarsa ta kyautata, ladansa zai yawaita, kuma rayuwarsa ta dadada, kuma kaunarsa ta wajaba[17].

B- Kyakkyawan Zato

59. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: wanda zatonsa ga mutane ya kyautata, to zai samu kauna daga garesu[18].

C- Kyakkyawar Dabi’a

60. Imam Ali (A.S) ya ce: Kyakkyawar dabi’a tana sanya kaunar juna, kuma tana karfafa soyayya[19].

D- Kyakkyawan Zamantare

61. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: kyakkyawar abotaka tana dada kauna a zukata[20].

62. Daga gareshi (A.S) ya ce: wanda ya kyautata abotaka, abokansa zasu yawaita[21].

f- Ikhlasin Kauna

63. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka tafiyar da al’amuran makiyinka, ka kuma yi ikhlasi ga masoyinka, ka kiyaye ‘yan’uwantaka kuma ka kare mutunci[22].

G- Sakin Fuska

64. Imam Ali (A.S) ya ce: Sakin fuska igiyar soyaya ce[23].

65. Daga gareshi (A.S) ya ce: sakin fuska sababin soyayya ne[24].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next