Sabuban Soyayya



K- Neman tsarin Allah

102. Imam zainul abidin (A.S): Ubangiji ka sanya soyayyata a zukatan bayinka… kada ka sanya mu daga gafalallu, ka so ni, ka sanya sona, ka soyar da ni abin da kake so na zance da aiki; har sai na shiga cikinsa da jin dadi[62].

103. Littafin manla yahadhuruhul fakih: ya kasance daga wasiyyar Manzon Allah (S.A.W) ga Ali (A.S): ya Ali, idan ka nufi wani birni ko wata alkarya yayin da ka ganta ka ce: ya Ubangiji ni ina rokon ka alherinta, ina kuma neman tsarinka daga sharrinta, ya Ubangiji ka soyar da mu gun ahlinta, kuma ka sanya son salihan ahalinta garemu kuma [63].

3 / 6

Abin Da Yake Wanzar Da Kauna

Kur'ani:

“Masoya a wannan rana sashensu makiya ne ga sashe, sai dai masu takawa”[64].

Hadisai:

104. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ‘yan’uwa saboda Allah madaukaki soyayyarsu tana dawwama; saboda dawwamar sababinta[65].

105. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Son ‘yan duniya yana yankewa; saboda sababinsa yana yankewa. Son ‘yan lahira yana dawwama; saboda dawwamar sababinsa[66].

106. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Kyakkyawan zama yana dawwamar da kauna[67].

107. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Ka tausasa tafinka; domin duk wanda ya tausasa tafinsa to zai dawwamar wa mutanensa soyayyarsa[68].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next