Kasuwanci Da Aure Da Albishir



e)Zai tunatar da mutane abin da Isa (A.S) ya gaya musu

f) Kuma zai yi shaida ga Masih Isa (A.S)

2.Hijirar Yahudawa da Kiristocin yankin larabawa musamman Madina da Khaibar domin samun da suka yi a littattafansu game da siffofin annabin karshe cewa zai zauna a wannan yankuna ne, sai suka yawaita hijira domin kwadayin ya zama su suka haife shi.

3.Samun yaduwar labarin cewa zai zo a yankin larabawa, al’amarin da ya sanya yawaitar kiristoci masu bauta suka warwatsu a yankuna daban-daban na jazirar larabawa domin jiransa da biyayya gareshi idan ya bayyana.

4.Yaduwar labarin bayyanarsa a ko’ina a kasashe al’amarin da ya sanya wasu mutane yawon neman kasar da zai bayyana, kamar Madina da Makka, kuma misalin irin wadannan mutane da suka shahara akwai Salman Farisi.

5.Abin da mai bauta Bahira ya gaya wa Abu Talib da ya koma da shi gida, yayin da ya yi tafiya da shi fatauci yana yaro. Bahira ya gaya masa idan yahudawa suka gano shi zasu kashe shi domin hassadar cewa ba a haife shi daga tsatson su ba. Bahira ya tabbatar wa Abu Talib (A.S) cewa ba shi ne babansa ba, domin ba za a haife shi ba sai bayan wafatin babansa (A.S).

Wannan yana nuna mana irin yadda siffofin annabi suka zama sanannu a wannan yankuna ta yadda har yaruntarsa ba ta iya dusashe wannan siffofin ba da masu bauta a dazuka da tsaunuka irin su Bahira suka iya gano shi tun yana karami. Kuma wannan yana nuna tsananin kishirwa da sanin zuwansa da yake tattare da jama’ar wannan zamanin musamman Yahudawa da Kiristoci da larabawan wadannan yankunan.

Marubuci: Hafiz Muhammad Sa'id

www.hikima.org

hfazah@yahoo.com

[1] - Assiratul muhammadiyya: 41.

[2] - Almusdapha min siratil musdapha: 58.

[3] - A’alamul hidaya: 1/67.

[4] - Sahih Muslim: 7/134. Sahih buhari: 5/39.

[5] - Injilar Yohana: Assihah 14. Wato John: Genesis 14.



back 1 2 3