Kasuwanci Da Aure Da AlbishirHaka nan ne ya aure ta (A.S) aka kafa gida mai haske cike da shiriya. Manzo (S.A.W) yana fadi game da ita: Khadiza (A.S) ta yi imani da ni yayin da mutane suka kafirta da ni, ta gaskata ni yayin da mutane suka karyata ni, ta taimake ni da dukiyarta yayin da mutane suka hana ni, kuma Allah ya arzuta ni â€کya’ya da ita ya hana ni â€کya’yan mutane (ta wata matar)[4]. AlbishirDa Zuwan Manzo (S.A.W)
Hakika an samu albishir da zuwan manzo (S.A.W) tun kafin zuwansa da shekaru masu yawa kamar yadda yake a sunnar Allah ta yin albishir da wani babban abu ga mutane tun kafin zuwansa. Daga cikin inda aka samu albishir da zuwan manzo (S.A.W) akwai: 1.Injil; Yohana: “Idan kun kasance kuna so na to ku kiyaye wasiyyata, ni zan nema daga Uba sai ya ba ku wani abin yabo (Ahmad), domin ya zauna tare da ku har abada[5]. A cikin wannan fakara ya ci gaba da cewa: “Ba zan yi muku magana da yawa ba; domin shugaban wannan duniya yana tafeâ€‌. Kuma ya ce: “Amma abin godewa ruhi mai tsarki da baban zai aiko shi da sunana, shi ne zai sanar da ku komai, kuma zai tunatar da ku dukkan abin da na gaya mukuâ€‌. Da sauran abubuwan da suka zo game da hakan. Idan mun lura zamu ga cewa: a)Annabi Isa (A.S) ya yi bishara da wanda zai zo bayansa b) Zuwansa an shardanta shi da tafiyar shi Annabi Isa (A.S) c)Kuma Allah ne zai aiko shi d) Ya san komai
|