Kasuwanci Da Aure Da Albishir



Kasuwancinsa

Kasancewar gidan Abu Talib yana da karancin yalwa wannan ne ya sanya manzo (S.A.W) ya motsa domin ganin ya dauki nauyin wannan gida, ta hanyar karbar kwadagon kasuwanci na fatauci kamar yadda yake al’amari sananne a wannan zamani.

Manzo ya yi fatauci da dukiyar Khadiza (A.S) da shawarar Abu Talib (A.S), kuma wannan ya samu alheri da yawa da albarka da ba ta lissafuwa.

Sai ya yi fatauci zuwa Sham da dukiyarta ya dawo yana mai cike da hannu mai albarka da kuma amana da ba ta taba gani ba. Musamman daga labaru da ta samu daga mutane daban-daban kamar bawanta Maisara.

Annabi mai girma ya bayar da dukkan ribar da ya samu na hakkinsa na fatauci ga amminsa Abu Talib gaba daya domin yalwatawa ga iyalansa, wannan al’amari ya sanya shi farin ciki mai yawa da abin da dan dan’uwansa Muhammad (S.A.W) ya yi masa na kyauta[1].

Aurensa

Manzon Allah (S.A.W) ya auri mace mafi kamala a cikin larabawa da mafi yawa daga manyan Makka sun so aurenta amma ta ki amincewa da su saboda kamalarta da kuma yanayinsu na ba tsararrakinta ba ne su a halaye.

Musamman ma wasu suna sonta ne domin wani abu na duniya da take da shi kamar kyawunta ko dukiyarta, wasu kuma ma’abota dukiya maras misali ne amma duk da haka taki amincewa, sai ta yarda da neman da Abu Talib (A.S) ya yi daga gareta na aure da dan dan’uwansa Muhammad, kuma ta amsa masa abin da ya nema, domin kamalarsa da kuma darajar gidansu a cikin larabawa da kuma kamewar Manzo (S.A.W) da rikon amanarsa.

Khadiza (A.S) ta auri Manzo (S.A.W) tana budurwa a lokacin ba ta taba aure ba, tana â€کyar shekara goma sha takwas, shi kuma yana dan shekara ishirin da biyar[2].

Abu Talib (A.S) ya tafi wajan amminta Amru Dan Asad ya nemi aurenta ga manzo (S.A.W), domin an kashe babanta kafin wannan lokacin.

Abu Talib (A.S) yana cewa a yayin da ya tafi neman aurenta ga Manzo (S.A.W): “Godiya ta tabbata ga ubangijin wannan daki (na ka’aba), wannan da ya sanya mu daga tsatson Ibrahim (A.S) da kuma zuriyar Isma’il (A.S)… sannan dan dan’uwana… -yana nufin manzon Allah- ba a auna shi da wani mutum daga kuraishawa a sikeli daya sai ya yi rinjaye, kuma ba a kwatanta shi da wani mutum sai ya fi shi daukaka, … ga shi yana son Khadiza (A.S), mun zo muna neman aurenta a wajanka, da yardarta da kuma umarninta, kuma sadakin yana kaina a dukiyata da zaku nema hannu-da-hannu ko kuma ajalan –na rantse da ubangijin wannan Dakin na Ka’aba- (wannan aure) rabo ne mai girma, addini mai yaduwa, kuma ra’ayi cikakkeâ€‌.

Sai Muhammad (S.A.W) ya tashi domin ya tafi tare da Abu Talib (A.S) gida, sai Khadiza (A.S) ta ce da shi: ina zaka tafi, ai gidana gidanka ne kuma ni mai hidimarka ce[3].



1 2 3 next