Ayyuka da Sakamako



A-Manzo (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya rasu kuma ana binsa azumi, sai babban dansa ya rama masa a madadinsa.[10]

B-Ibn Abbas yana cewa: wata mata ta zo wajen Manzo (s.a.w) sai ta ce mahaifiyata ta rasu kuma akwai azumi a kanta.

Sai Manzo ya ce: Idan akwai bashi a kanta ke ce zaki biya? Sai wannan mata ta ce ni zan biya! Sai Manzo (s.a.w) ya ce: To biyan bashin Ubangiji shi ya fi muhimmanci.[11]

C-Wata mata ta zo wajen Manzo sai ta ce: Na ‘yantar da baiwa a madadin mahaifiyata. Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Ladar hakan zata isa zuwa gareta. Sai wanann mata ta kara da cewa, sannan kuma azumin wata daya yana kanta, shin zan iya yin wannann azumin a madadinta? Sai Manzo ya amsa mata da cewa; kina iya yin azumin. Sannan sai ta kara da cewa mahaifiyata ba ta yi aikin hajji ba, ina iya yin hajji a madadinta? Sai Manzo ya amsa mata da cewa kina iya yi.

2-Amfanar mamaci daga sadaka

Kamar yadda muka ambata cewa ruwayoyin da suka zo dangane da wannan suna da yawan da ba zai yiwu mu kawo dukkansu ba, amma a nan zamu kawo hadisi guda biyu kawai wadan zasu iya warware mana dukkan wannan matsalar.

A-A’isha tana cewa: Wani mutum ya zo wajen manzon Allah sai ya ce: Mahaifiyata ta rasu sannan kuma ba ta yi wasiyya ba, sannan ina tunanin cewa idan da har ta iya yin magana zata bayar da sadaka ne, yanzu idan na bayar da sadaka a madadin mahafiyata ladar zata je mata?

Sai Manzo (s.a.w) ya amsa da cewa me zai hana![12]

B-Sa’ad Bn Ubada ya kasance daya daga cikin sahabban Manzo, lokacin da mahaifiyarsa ta rasu, sai ya zo wajen manzon ya ce: wace sadaka ce tafi kowace daraja? Sai Manzo (s.a.w) ya amsa masa da cewa ta ruwa.

Sa’ad Bn Ubada sai ya gina rijiya ya ce wannan rijiya saboda maharfiyar Sa’ad. [13]



back 1 2 3 4 5 6 next