Ayyuka da Sakamako2-Wani lokaci kuwa ba shi da wani hannu sai dai kawai shi mumini ne. Dangane da kashi na farko kuwa wanda ya kasance mamaci yana da hannu a cikin ayyukan wanda yake raye babu wata magana a cikin wannan. Ya wadatar dangane da wannan mu saurari hadisin Manzo wanda duka bangarori guda biyu suka ruwaito shi. Abu hurera yana cewa Manzo (s.a.w) ya ce: “Idan mutum ya mutu dukkan ayyukansa sun yanke sai guda uku kawai; sadaka wacce take gudana, ko ilimi wanda ake amfana da shi, ko kuwa dan kwarai wanda zai yi masa addu’aâ€. [5] 1-Sadaka mai gudana ita ce kamar gina masallaci, asibiti makaranta da dai sauransu, wadanda mutane suke amfani da su. 2-Ilimin da mutane suke amfana da shi. 3-Dan kwarai wanda zai rika yi wa mutum addu’a. Idan mutum ya rasu zai ci gaba da amfana da wadannan abubuwa guda uku da muka ambata a sama, domin kuwa yayin da yake da rai yana da hannu wajen samar da wadannan abubuwa, kamar masallaci da ya gina lokacin da yake raye sannan yanzu mutane suna ci gaba da amfani da shi, ko kuwa littafi ya rubuta har yanzu mutane suna ci gaba da amfana da shi, ko kuwa ya haifi da sannan ya yi masa tarbiyya ta gari yana yi masa addu’a. Jarir Bn Abdullah yana cewa: Manzo (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya yi wata Sunna mai kyau a cikin addini sannan mutane suka yi aiki da ita bayansa, za a rubuta masa ladar wanda ya yi aiki da ita ba tare da an tauye ta wanda ya yi aikin ba. Haka nan duk wanda ya yi wata Sunna mummuna (wato ya yada wani abu da bai dace ba) a cikin addini sannan wasu suka yi aiki da ita, to yana da zunubin duk wanda ya aikata ba tare da an tauye zunubin wanda ya aikata hakan ba[6]. Saboda haka amfana da lada ko zunubin da wadanda suka riga mu zasu yi ta wannan fuskar ce, wannan kuwa saboda hannun da mamaci yake da shi wajen aiwatar da hakan yayin da yake raye, wato lokacin da yake raye ya bayar da gudummuwa wajen yada aikin assha ko kuma ya taimaka wajen yada aikin kwarai, domin idan da bai yi hakan ba mutane ba zasu samu damar aikita hakan ba. Tambaya zata kasance dangane da bangare na biyu ne wanda idan ya kasance mutum ba shi da hannu wajen ayyukan da wani mutum yake yi bayan rasuwarsa, shin wannan mamaci zai iya samu ladar aikin wannan rayayyen, amsar da Kur’ani da hadisi kuwa suka bayar dangane da wannan ita ce zai ya samu. Wannan amsa kuwa a takaice ita ce, idan mutum wanda yake da tsarkin zuciya ya nema wa wani mamaci gafara ga Ubangiji, ko kuma ya yi wani aiki a mai makon mamaci ko kuma ba da wannan niyyar ba, sai ya bayar da wannan lada ga mamaci a mastayin kauta, wannan ladar zata isa zuwa ga wannan mamacin. Kur’ani mai girma a wurare da yawa yana bayyanar da yadda mamata zasu iya amfana daga neman gafarar da wadanda suke raye suke musu kamar haka:
|