Ayyuka da SakamakoA-Neman Gafarar Mala’iku Ga Muminai Kur’ani mai girma a fili yake ya bayyanar da cewa mala’iku suna nema wa masu imani gafara a wajen Allah madaukaki. Idan har ladar hakan ba ta isa ga mamaci wannan neman gafarar da mala’ik suke zai zama marara ma’ana. Ga abin da Kur’ani yake cewa a kan haka: 1-Wadanda suke daukar al-arshi da na gefensa, suna tasbihi da godiyar ubangijinsu, kuma suna masu imani da shi, kuma suna neman gafar ga wadanda suka yi imani suna cewa ya ubangijimmu ka yalwatar da rahama da ilimi ga komai, kuma ka gafarta wa wadanda suka tuba, suka kuma bi hanyarka, katseratar da su azabar jahannam[7]. 2-“Ya rage saura kadan sama ta tsage daga bisanta, kuma mala’iku suna tasbihi da godiyar ubangijinsu, sanann suna neman gafara ga wadanda suke a bayan kasa, Ku sani Allah shi ne mai gafara mai jin kaiâ€[8]. Dangane da wadannan ayoyi guda biyu da suka gabata suna magana ne a kan neman gafarar da mala’iku suke yi wa muminai, amma aya ta uku zamu ga yadda muminai ne suke nema wa junansu gafara kamar haka: 3-“Wadanda suka zo bayansu, suna cewa, ya Allah a gafarta mana da ‘yan’uwammu wadanda suka riga mu da imani, kada sanya wani jin zafi cikin zuyarmu dangane da wadanda suka yi imani, ubangijimmu lallai kai mai tausayi ne kuma mai jin kaiâ€[9]. Wadannan ayoyi guda uku suna nuna mana yadda wadan suka riga mu suke amfana da neman gafarar wadanda suke raye suke yi musu. Sannan wannan amfanar da suke yi bai takaita ba da neman gafara kawai, ya hada da abubuwan daban-daban banda wannan, kamar yadda ruwayoyi suka bayyanar da hakan: Kyakkyawan Aiki Da Bayar Da Ladar Ga Wadanda Suka Rasu Dangane da kyautata wa wadanda suka rasu ruwayoyi da dama sun zo domin su bayyanar da hakan a cikin Littattafan hadisi, kuma dukkansu suna bayyanar da cewa idan mutum ya yi wani aikin lada a mai mai kon iyayensa, ko wani daga cikin dangi ko abokai to ladar zata je wa wanda aka yi saboda shi. Don haka a nan ya dace mu kawo wasu kadan daga cikin wadannan ruwayoyin. 1-Amfanar mamaci daga ladar azumi da hajji da aka yi a mai mai konsa
|