Rayuwa Bayan Mutuwa 3Wace jumla ta fi wannan bayyana inda Imam yake cewa ka tuna da mu a wajen Ubangiji ka kula da mu. [11] Wannan hadisi da kuma wasu hadisai masu yawa suna bayyana mana yadda mutum yake da alaka da wata duniya kuma wannan alakar tana ci gaba. Rayuwar Barzahu A Bakin Malaman Hadisi Da Fikihu Rayuwar barzahu tana daga cikin tushen akidar al’ummar musulmin duniya, Sannan manyan malamai wadanda suka yi rubutu a kan akida sun kawo wannan magana a cikin littafansu, sannan mu dauki wannan magana ta rayuwar barzahu wani abu ne wanda aka sallama a kansa. A nan kasa zamu yi nuni da wasu daga cikin maganganun wasu malamai da suka yi a kan hakan: 1-Ahmad Bn Hambal yana cewa: Azabar kabari gaskiya ce, Sannan zatambayi mutum a kan addini da Ubangijinsa, Sannan zai ga makomarsa aljanna ce ko wuta a cikin rayuwar barzahu. Sannan tamabayar kabari wacce mala’iku guda biyu zasu gabatar gakiya ce. [12] 2-Abu Ja’afar Dahawi (ya rasu a shekara ta 321) yana rubuta cewa: Mu mun yi imani da azabar kabari dangane da wanda ya cancanci hakan, haka nan dangane da tambayar da mala’iku guda biyu zasu yi wa mamaci a cikin kabari, dangane da Allah, addini da annabi, kamar yadda ya zo daga Manzo (s.a.w) 3-Abu hasan al-ash’ari (ya rasu a shekara ta 324) yana rubutawa a wata risala da ya yi dangane da akida, yana cewa: Mun yi imani da azabar kabari, tafkin alkausara, da mizani, siradi, tayar da matattu. 4-Bazdawi (ya rasu a shekara ta 331Bh) yana rubuta cewa: Tambayar kabari gaskiya ga AhlusSunna sannan mumini yana iya amsa wannan tambaya. 5-Imam razi a cikin tafsirin ayar da take cewaâ€suna albishir ga wadanda ba su riske su ba) yana ccewa: wannan tana ba da sheda a kan rayuwar mamaci a barzahu kafin ranar tashin kiyama. Haka Manzo yana cewa: Kabari lambu ne daga cikin lambunan aljanna, ko kuma rijiya ce daga cikin rijiyoyin gidan wuta, wannan shi ma wani dalili ne a kan hakan. Sannan yana karawa da cewa: Hadisan da suka zo dangane da tambaya da azabar kabari kusan mutawatirai ne.
|