Rayuwa Bayan Mutuwa 3



Sannan abin da yake shaidawa a kan wannan ma’ana a bayyane shi ne, Allah madaukaki ya sanya hanyoyi guda biyu a gaban Manzo (s.a.w) a aya ta uku mai zuwa inda take nuna hanya ta uku yana cewa:

“Kuma lallai mun bai wa Musa (a.s) alamomi guda tara bayyanannu, sannan ka tambayi Bani Isra’ila yayin da ya zo Musa ya zo musu, sai Fir’auna ya ce masa lallai Musa ina ganinka dandabo”.[7] A cikin wannan aya maganar ta zo ne daga su Bani Isra’il ba wai wasu gungun malamai ba wadanda suke karanta littafai. Saboda haka ba tare da wata hujja ba babu yadda zamu yi tawili dangane da aya ta uku.

Na biyu: Aya ta farko tana nufin cewa a tambayi dukkan annabawa da suka gabata, hada da Nuhu da Ibrahim… Amma aya ta biyu kuwa tana magana ne a kan malaman yahudu da nasara, ta yadda ta hanyar karatun da suke suna iya amsa tambayar Manzo dangane da umurnin da Allah ya bai wa manzanninsu, ta yadda zasu gabatar da wannan ga Manzo da al’ummarsa. Saboda haka a nan ba mu da hakkin da zamu takaita ma’anar wannan aya ta farko ga malaman yahudu da nasara kawai. Wato; alkawarinsu ya takaita ne kawai ga annabawansu ba hada ba da sauran annabawa.

Na uku: Aya da ake magana a kanta, ta zone a cikin surar Zukhruf, wannan sura kuwa kamar yadda malaman tafsiri suka hadu a kan cewa ta sauka ne Makka, haka nan ma’anarta ma tana tabbatar da hakan. Saboda haka a garin Makka a wannan lokaci babu wasu malaman yahudu da nasara ko wasu gungun mutane masu yawa ta yadda Manzo zai tambaye su.

Rayuwar Barzahu A Cikin Hadisai

Bahasimmu a cikin Kur’ani dangane da wannan magana ya kawo karshe. Alakar kuwa da take akwai tsakanin wannan duniyar da duniyar barzahu hadisai da dama sun zo da bayanin hakan, saboda haka a nan saboda mu takaita zamu wadatu da wasu tabbatattun hadisai a matsayin misali a kan hakan:

1-Manzo (s.a.w) ya yi magana da wadanda aka kashe a yakin “Badar”

Bayan yakin Badr ya kawo karshe, a lokacin kafiran kuraishawa aka kashe musu mutum saba’in aka kuma kama wasu saba’in din a matsayin bursunonin yaki, saura kuwa suka ranta a cikin na kare. Manzo mai girma (s.a.w) ya bayar da umarni, aka zuba wadanda a kashe daga kuraishawa a cikin wata rijiya, a lokacin da a ka zuba su a cikin rijiya sai Manzo ya kira kowane daya bayan daya da sunansa ya ce: Ya kai Utba, Shaiba, Umayya, Abu Jahl…shin kun samu abin da Allah ya yi muku alkawari?! Ni kam na samu abin da Allah ya yi mini alkawari ya kasance kuma gaskiyane. A wannan lokaci sai sai wasu gungu daga cikin musulmai suka ce wa Manzo, kana kiran wadanda suka mutu ne?! Sai Manzo ya amsa da cewa: Ai ba ki fi su jiba Amma su ba su iya amsawa.

Ibn Hisham yana cewa: A lokacin nan sai Manzo ya kira wadanda aka kashe daga kafiran kuraishawa ya ce: Ku wadan ne irin mummunan dangi kuka kasance ga Manzo?! Kuka karyata ni, a lokacin da wasu suka gasgata ni, lokacin da wasu suka ba ni mafaka, amma ku kuka yake ni, amma sai wasu suka taimake ni. Shin abin da Allah ya yi muku alkawari kun same shi?!

Wannan magana da Manzo ya yi da wadanda aka kashe daga cikin kafiran kuraishawa wani abu wanda dukkan bangarori guda biyu suka kawo, wato malaman Shi’a da Sunna sun ruwaito wannan al’amari. Sannan a kan wannan zamani ma sun ruwaito wannan abu a cikin wakokinsu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next