Rayuwa Bayan Mutuwa 3



Manzo (s.a.w) ya yi magana a kan wadanda suke irin wannan aiki yana cewa: “Duk wanda ya fassara Kur’ani da ra’ayinsa, to ya tanaji wurin zamansa a cikin wuta”.

Tambaya: Annabi Salihu ya yi magana ne da mutanen da suka yi saura, wato wadanda suka yi imani da shi, sakamakon haka ne suka tsira.

Tsammanin haka mai rauni ne, sannan ba shi da ma’ana, domin idan yana magana ne da masu imani wadanda suka yi saura daga cikin mutanensa, to me ya sa a gaba yake cewa: Sai dai ku ba ku son nasiha”.

2- Shu’aib, inda yake magana da ruhin mutanensa

“Girgizar kasa ta kama su, suka wayi gari a cikin gidajensu suna halakakku”.[2] “Su ne wadanda suka karyata Shu’aibu sun kasance kamar ba su rayuwa ba a ciki, Wadanda suka karyata Shu’aibu sun kasance sun yi asara”.[3] “Sai ya juya musu sai ya ce: Yaku mutane ku sani na isar muku da sakon Ubangiji, sannan na yi muku nasiha, to yaya zan ji tausan mutanen da suke kafirai”?[4] Yanayin kafa hujja da wannan aya ya yi yanayi daya da yadda aka kafa hujja da shi a cikin magana a kan Salihu (a.s).

3-Manzo (s.a.w) ya kasance yana magana da ruhin annabawa

“Ka tambayi wadanda muka aika kafinka daga manzanimmu, shin mun sanya wani bayan Rahaman a matsayin abin bauta”?[5] Zahirin wannan aya tana nuna cewa Manzo yana iya magana da annabawan da suka gabata, kuma suke rayuwa a wata duniya, ta yadda zai tambaye su, ta yadda yana nuna rashin hanuwa a kan hakan ta hanyar hankali, saboda haka babu wani dalili da zai sanyamu ki yin amfani da zahirin wannan aya.

Tambaya: Abin da ake nufi da wannan aya shi ne ana tambayar yahudawa da nasara ne, kamar yadda a wata aya yake cewa: “Idan kana shakku a kan abin da muka aiko maka, ka tambayi wadanda suke karanta littafin da aka saukar kafinka, tabbas gaskiya ta zo maka daga ubangijinka”.[6]

Amsa: wanann tsammani yana da rauni kwarai da gaske saboda:

Na farko: Tafsirin aya da wata aya yana zama daidai yayin da aya ta farko ta zamanto ba a bayyane take ba, amma idan ayar ta kasance ba ta da wani kokwanto ko rashin bayyana, ba bu wani dalili da zai sanya a dauki hannu daga zahirinta a yi tawilinta, ta yadda zamu ce: ai ma’ana shi ne a nan tambaya ne ga malaman yahudu da nasara, domin kuwa babu wani wanda zai hana Manzo ya tambayi dukkan wannan gungu guda biyu, domin kuwa musamman aya ta farko tana magana ne da Manzo in da take nuna cewa ya tambayi annabawan da suka gabata, amma aya ta biyu tana magana ne da al’ummar Manzo inda take nuna su tambayi malaman yahudu da nasara.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next