Halayen Manzon Allah (s.a.w)Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makka a lokcin akwai jama'a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da sakon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: "Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta"[4]. A lokacin tunda mutanen Makka mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka rika yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa'adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: "Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni"[5]. Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane kalilan, na farkonsu Imam Ali sannan sai matarsa Hadiza (a.s) sannan sai wasu mutane. Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali (a.s) sannan daga mata sai Hadiza (a.s). Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madina wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai karfinsu ya dadu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari'arsa mai sauki mai hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madina har suka fi dukkan duniya da addini na sama da wadanda ba na sama ba. Kuma an samu yakoki masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin wadanda ake kashewa daga bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu, wato; wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba. Tun lokacin da aka aiko Annabi da sako har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (a.s) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Kur'ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (s.a.w) ya yi umarni da a hada shi kamar yadda yake a yau din nan. Manzo (s.a.w) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu'amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu. Bayan cikar addini da kafa Ali dan Abu Dalib (a.s) shugaba na al'umma kuma halifa bayan Annabi (s.a.w) wannan kuwa ya faru a ranar Gadir ne goma sha takwas ga zulhajji a shekarar hajjin bankwana sai Allah ya saukar da ayar: "A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni'imata gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini"[6]. Sai Annabi ya yi rashin lafiya mai sauki, sai dai ya yi tsanani har sai da ya hadu da Ubangijinsa a 18 ga watan safar na 11H. Kuma wasiyyinsa halifansa Imam Ali (a.s) shi ne ya yi masa wanka da salla da binne shi a dakinsa a Madina inda kabarinsa yake yanzu.
|