Halayen Manzon Allah (s.a.w)Manzon Allah (s.a.w) ya kasance bai taba cewa da mai yi masa hidima don me ka yi kaza ba, sai dai ya ce; da ka yi kaza da ya fi. Yana kiran kowa da kinayarsa domin girmamawa, yana sanya kinaya ga maras kinaya, yana ba wa wanda ya shigo matashinsa, idan kuwa ya ki sai ya nace masa har sai ya karba, yana futowa bayan bullowar rana, domin yana yin addu'a ne tsakanin alfijir da bullowar rana, idan ya shiga gida sai ya zauna a farkon wurin da ya samu a kowa. Ya kasance bai taba yi wa kowa magana gwargwadon hankalinsa ba, sai dai gwargwadon hankalin su mutanen domin tausaya musu, shi mai yawan rusunawa da roko ga Allah ne, mai yawan addu'a, yana yanke akaifarsa, yana rage gashin baki kafin ya fita sallar juma'a, yana yin raha don tausaya wa al'ummarsa domin kada wasu su wuce gona da iri a kansa su rike shi kamar yadda kirista suka riki Isa (a.s). Yana yi wa na kusa da shi magana da abin da ya dace da su, idan suna maganar lahira sai ya yi tare da su, idan ta duniya ce sai ya yi tare da su, idan suka ci ko suka sha sai ya kasance tare da su. Ba ya duba na ha'inci zuwa ga abin da bai halatta ba, ko nuni da hannu haka nan, idan ya yi magana sai ya maimaita sau uku domin mai ji ya fahimta kuma ya fahimce shi ko ya isa da shi ga mutanensa. Idan aka tambaye shi yin wani abu; idan zai yi sai ya ce; Na'am, amma idan ba zai yi ba sai ya yi shiru, ba ya kallon abin da yake na shagaltuwar duniya domin kada ya shagaltu da shi ko ya dauke masa hankali, kuma idan wani abu ya bata masa rai sai ya shiga yin salla, yana son kebewa shi kadai domin yin ambaton Allah da tunani da lura shi kadai, yana tanadar ruwan sallar darensa, yana tamaka wa matansa ayyukan gida, yana yanka nama, baya kura wa wani ido, yana sanya zoben azurfa a hinsar na dama, yana yin aswaki, yana raka janaza, yana gaida maras lafiya, ba ya tsawaita salla idan wani yana jiran sa sai ya gama salla ya ce masa: Kana da wata bukata ne?
|