Halayen Manzon Allah (s.a.w)



Idan muka koma batun sha zamu ga yana sha a kwano, kuma yana sha bayan ya ambaci Allah sannan idan ya kare sai ya gode masa, yana zukar ruwa ne ba ya kwankwandarsa, kuma ba ya lumfashi a cikin kwanon shan ruwa, idan zai yi lumfashi sai ya yi nesa da kofi ko kwanon shan ruwan.

Sannan akwai matakai masu mihimmanci bayan ci kamar kurkure baki, da muka fi sani a  yau da yin burush kafin mutum ya kwanta domin kada abin da ya bari na kufan abinci ya lalata masa hakora, da sauran matakan tsafta da mai aminci ya yi nuni da su a aikace.

An ruwaito daga gareshi mai aminci cewa: Ka ci kana sha'awa, ka bari kana sha'awa. Wannan lamarin yana nuna mana muhimmancin rashin cika ciki ya yi yawa, don haka riko da wadannan nasihohi nasa mai aminci shi ne hanyar da zai samar da lafiya ga al'umma.

Akwa maganganun masu yawa a wannan babin da suka hada da abubuwan da  ya kamata a ci, da lokacin da ya kamata a ci, da zamanin da ya dace da cin su, da kuma abubuwan da bai kamata a ci ba, da amafanin abubuwan ci daban-daban, sai dai zmau takaita a nan zuwa wani jikon.

Amma idan muka duba adon manzon Allah (s.a.w) zamu ga ya ba wa wasu abubuwa muhimmanci kamar turare.  Imam Jafar Sadik (a.s) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana kashe wa turare kudi fiye da yadda yake kashe wa abinci. Kuma ba a ba shi wani turare sai ya sanya shi yana cewa: Shi kanshinsa mai dadi ne, daukarsa mai sauki ce, kuma ya kasance yana yin turare da almiski. Kuma a cikin duhun dare ana iya gane shi da kanshin turarensa kafin a gan shi, don haka idan ya wuce sai a ce; wannan manzon Allah ne (s.a.w).

Ya kasance yana taje gashin kansa da gemunsa da matajin karfe ko na katako, kuma matansa suna taje masa gashinsa da gemunsa, sai su dauki gashin da ya fadi kasa, kuma sau da yawa yana taje gemunsa sau biyu a rana. Ya kasance yana son gyara gashi yana kin buja-buya, yana farawa da kai sannan sai gemu sai kuma sauran inda yake da gashi.

 Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana shafa mai, kuma yana farawa da girarsa sannan sai gashin baki, sai kansa sai gemu. Kuma yana sanya kwalli sau uku a dama sannan sai hagu sau biyu, kuma yana sanya kwalli har a lokacin azumi.

Ya kasance yana duba madubi, yana kuma duba ruwa ya gyara keyarsa, yana ado ga sahabbansa balle ga matansa. Yana cewa: Ubangiji yana son bawan da idan zai fita cikin mutanensa ya shirya musu ya yi musu ado.

Amma sunnonnin manzon Allah (s.a.w) a wannan lokacin musulmi sun yi wurgi da mafi yawancinsu, sai suka dauki wani abu daban ba su ba, aka jefar da mafi yawan dabi'unsa da halayensa, aka musanya su da wasunsu, sai musulmi suka musanya kaskan da kansa da girman kai da dagawa, kyawawan halayensa kuwa aka wurga su kwandon shara aka dauki munanan halaye aka yafa.

Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana kallon kasa-kasa yayin tafiya, yana fara wa wanda ya hadu da shi da sallama, ba ya magana sai gwargwadon bukata, yana girmama ni'imomin Allah ba ya rena komai daga garesu, sai ya gode wa Allah madaukaki, yana dariya amma ta murmushi, yana tambayar sahabbansa idan bai ga dayansu ba, yana tambayar mutane don ya san halinsu, yana tashi da zama bisa ambaton Allah, yana zama inda ya samu wuri ne, yana girmama abokan zamansa ba tare da ya nuna fifiko ba, ba ya hana wanda ya roke shi sai dai iban babu sai ya yi masa magana mai dadi ko addu'a ko ya yi masa nuni da inda zai samu bukatarsa, ba ya jayayya da nuna isa kan wasu don wulakanta su, ba ya hassada ko kullata, yana barin abin da babu ruwansa, ba ya yanke wa wani maganarsa, yana daidaita kowa a kallo, ya fi kowa fasaha, yana magana mai tattare da hikima, yana da yawan kunya, ya fi kowa karfi da jarumta, yana kuka don tsoron Allah, yana tuba da istigfari sau 70 a kowace rana, yana zama da talakawa, yana ci da miskinai, yana sadar da zumunci, yana dinke tufafinsa, yana gyara takalmansa, yana ci kamar yadda bayi suke ci, yana zama a kasa, yana hannu da talaka da mai kudi, ba ya wulakanta talaka don talaucinsa, yana sallama ga kowa talaka da mai kudi, babba da yaro, yana kallon mudubi, yana zabar mafi tsanani don saba wa ransa da saba wa son rai, yana cin gabansa, ba ya ci yana kishingide, yana sha da lumfashi uku, yana son yin abu da hannun dama; damansa domin abinci, hagunsa domin jikinsa, idan ya yi magana sai ya yi murmushi, mafi yawan zamansa yana kallon alkibla ne, idan aka zo da yaro sai ya yi masa addu'a ya kai shi dakinsa, kuma tayiwu yaron ya yi masa fitsari a daki sai ya bari sai mutanen sun tafi sai ya wanke da kansa, ba ya bari wani ya tafi tare da shi idan yana kan abin hawa sai dai idan mutumin zai hau tare da shi (wato manzon Allah ya goya shi kan dabba), idan kuwa mutumin ya ki hawa sai ya ce masa: Yi gaba sai ka same ni a wurin da kake so. Kuma ya kasance idan bai ga mutum kwana uku ba sai ya tabamya, idan ba ya nan ne sai ya yi masa addu'a, idan yana nan sai ya kai masa ziyara, idan maras lafiya ne sai ya je ya gai da shi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next