Mukamin Ahlul-bait[19] Jumlar "....ku yi salati a gare shi.." wacce ta zo cikin ayar tana nuni da wajibci ne, don malaman Usul al-Fikh sun bayyana fi'ilin umurni a matsayin yana nuni ga wajibci ne, wasu ma suna ganin cewa a duk lokacin da fi'ilin umurni ya zo cikin Alkur'ani ko hadisi yana nuni ga wajibci ne sai dai idan akwai wani abin da yake nuni da cewa wajibcin ya koma zuwa ga mustahabi. [20] Tafsirul Kabir na Fakhrurrazi a tafsirin Surar Ahzab aya ta 56. [21]Almizan fi Tafsiril Kur'an na Allamah Tabataba'i, juzu'i na 16, shafi na 344. [22] Allamah Hilli wanda ya kasance daga cikin manyan malaman fikihun mazhabar Ahlulbaiti (a.s), kuma yana daga cikin sanannun karni na bakwai bayan hijira, yayin da yake ambaton wajiban salla yana cewa: (Na bakwai) tahiya, wajaba ce a dukkan salla mai raka'o'i biyu sau guda, sannan kuma sau biyu a salloli masu raka'o'i uku da hudu, da mutum zai bar ta da gangan, to salla ta vaci. [23] Zamakhshari cikin littafin al-Kashshaf, yayin tafsirin Surar Insan, haka nan kuma Fakhrurrazi shi ma ya kawo wannan ruwaya cikin littafinsa na Tafsir al-Kabir . Haka ma Tabrisi cikin Majma'ul Bayan. [24] Birnin Makka ya fuskanci fari mai tsananin gaske kafin aiko Ma'aiki (S.A.W), don haka sai Manzon Allah (S.A.W) ya dauko Imam Ali (A.S) daga wajen mahaifinsa Abu Talib (A.S) zuwa gidansa don yi masa tarbiyya da kuma saukaka wa Baffansa (Abu Talib) wanda ya kasance fakiri ne. [25] Zamakshari cikin al-Kashshaf yayin tafsirin Surar Ma'ida aya ta 55. [26] Al-Wahidi cikin Asbabun Nuzul / Surar Ma'ida aya ta 55. [27] Mai son karin bayani sai ya koma ga..... [28] Hakim al-Haskani cikin littafin Shawahid al-Tanzil juzu'i na 1 shafi na 190 ya ruwaito cewa:"Daga Abdulla bn Abi Aufa, yana cewa: Na ji Manzon Allah (S.A.W) ya karanto wannan aya (sai ya karanto ayar Tabligh) a Ranar Ghadir Khum, sai ya daga hannayensa har ana ganin farin hammatansa, ya ce: "Ku sani duk wanda ya zamanto shugabansa, to Aliyu shugabansa ne". Haka nan ma Al-Wahidi cikin Asbabun Nuzul shafi na 135, da kuma Suyudi cikin Durrul Mansur juzu'i na 2 shafi na 198, daga Abi Sa'id al-Khudri cewa: Wannan aya ta sauka ne dangane da sha'anin Aliyu bn Abi Talib.
|