Mukamin Ahlul-bait



A ciki Durrul Mansur na Imam Suyudi, Abdurrazak da Ibn Abi Shaiba da Ahmad da Abd bn Humaid da Bukhari da Muslim da Abu Dauda da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ibn Mardawihi, daga Ka'ab bn Ujrah, ya ce wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, mun san yadda ake maka sallama, to ya ya ake maka salati? Sai ya ce: "Ka ce: Ya Allah Ka yi tsira a kan Muhammadu da Alayen Muhammadu kamar yadda Ka yi tsira kan Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai ne Abin godiya, Mai girma".

Malamin ya kawo hadisai goma sha takwas ban da wannan hadisin dukkan su suna nuni ga tarayyar Alayen Manzon Allah (S.A.W) da shi cikin salati. Ma'abuta littattafan hadisi sun ruwaito su daga sahabbai daban-daban. Ga wasu daga cikinsu: Ibn Abbas da Dalha da Abu Sa'id al-Khudri da Abu Huraira da Abu Mas'ud al-Ansari da Buraida da Ibn Mas'ud da Ka'ab bn Umrah da Ali (A.S). Sannan kuma a cikinsa Imam Ahmad da Tirmizi sun fitar da hadisi daga Hasan bn Ali (A.S) cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a gurinsa bai mini salati ba([21])".

Kamar haka ne malaman fikihu suka ruwaito wajibcin salati ga Annabi Muhammadu da Alayensa (A.S) cikin tahiyar salla([22]) da wajibcin kawo ambaton Alayen Muhammadu cikin salla.

Duk wanda ya sa ido a kan wannan aya zai fahimci cewa manufar shar'anta salatin da lizimtar da shi shi ne girmama Alayen Manzon Allah (S.A.W), wadanda Allah Ya tafiyar da dauda daga gare su kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa, domin al'umma ta yi koyi da su, ta bi tafarkinsu, kuma ta fake a gare su lokacin fitinu da sassabawa.

To wadannan da salla ba ta inganta sai gami da an masu salati, su ne Shuwagabannin al'umma, su ne a ka yi nuni da su kuma aka lamunce a yi koyi da su. Ba don tabbata da lamuncewar tsayuwarsu da kubutar abin da ya fito daga gare su ba, da Allah bai umurci musulmi a dukkan zamunna da su rataya da su da yi musu salati cikin kowace salla ba.

Hakika cikin wannan maimaitawa - maimaita salati ga Annabi da Alayensa, da kuma farlanta hakan a kowace salla - akwai jaddadawa da jan hankulan musulmi cikin kowace salla saboda muhimmanci Ahlulbaiti (a.s) da matsayinsu, da kuma koyi da su da rayuwa bisa tafarki da hanyarsu.

Ta Biyar: Surar Insan "Hakika mutane na gari suna sha daga wani kofin (giya) da mahadinta ya kasance mai kamshin kafur ne.

Akwai abubuwa guda biyar a cikin ko wane daya daga cikinsu da suka kasance wajibai, su ne kuwa: zama gwargwadon tahiya, yin shahadojin nan guda biyu da salati ga Annabi da Alayensa (A.S). Dubi Shara'ii Islam, juzu'i na 1, babin salla.

 (Shi kafur din) wani marmaro ne da bayin Allah suke sha daga gare shi suna bubbugo shi bubbugowa ta hakika. (Don ko) suna cika alkawari na bakance suna kuma tsoron ranar da sharrinta ya kasance mai tartsatsi ne. Suna kuma ciyar da abinci tare da kuma suna son sa; ga miskini da maraya da kuma ribatacce a yaki.

(Suna cewa): "Mu kawai muna ciyar da ku ne saboda Allah, ba ma nufin sakamako ko godiya daga wurinku. Hakika mu muna jin tsoron rana mai sa daure fuska matsananciya daga Ubangijinmu". Sai Allah Ya kare su (daga) sharrin wannan ranar Ya kuma hada su da haske da kuma farin ciki. Ya kuma saka musu da Aljanna da alhariri saboda hakurin da suka yi. Suna masu kishingida a cikinta a kan gadaje ba sa samun zafin rana ko sanyi a cikinta. Inuwowinta suna kusa da su, an kuma yiwo kasa-kasa da 'ya'yan itacenta kasa sosai. Ana kuma kai-ka-wo da korai na azurfa da kofuna wadanda suka kasance na karau. Karau din na azurfa ne, sun auna su, aunawa daidai da bukata. Ana kuma shayar da su wata giya a cikinta wadda mahadinta ya kasnce mai kanshin zanjabilu ne (watau citta mai yatsu). (Shi zanjabilu) wani marmaro ne a cikinta da ake kiran sa Salsabilu. Samarin hadimai dawwamammu da ba sa tsufa kuma suna kai-ka-wo tsakaninsu, idan ka gan su sai ka yi tsammanin su wani lu'u-lu'u ne wanda aka baza. Idan kuma ka yi kallo a canza ka ga ni'ima da kuma mulki kasaitacce. A samansu akwai tufafi sakar alhariri koraye da kuma abawarsa, aka kuma yi musu ado da warawarai na azurfa, Ubangijinsu kuma Ya shayar da su abin sha mai tsafta. Hakika wannan ya kasance sakamako ne a gare ku, kuma aikinku ya kasance abin godewa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next