Mukamin Ahlul-bait



[10] Rafdhu a wajen malaman Ahlussunna shi ne yarda da cewa Imam Ali bn Abi Talib (A.S) shi ne halifan Manzon Allah (S.A.W) na farko bayan rasuwarsa. Kuma Rafidhi shi ne wanda ya yarda da hakan.

[11] Fakhrurrazi cikin Tafsirul Kabir, yayin tafsirin Surar Shura aya ta 23.

[12] Ihya'ul Mait bi fadha'il Ahlilbaiti na Suyudi shafi na 8, kuma Suyudin ya ruwaito shi cikin Durrul Mansur , juzu'i na 6 shafi na 7 ta hanyar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, sannan kuma Dabarani ma ya fitar da shi cikin Mu'ujamul Kabir, juzu'i na 1 shafi na 125. Haka ma Tabari ya ruwaito shi cikin Zakha'ir shafi na 25, yana cewa: "Ahmad ya fitar da shi cikin Munakib. Kamar yadda kuma Ibn Sabbag al-Maliki ya ruwaito shi daga Nabawiy daga Ibn Abbas, shafi na 29. Hakan nan kuma Kurdabi ya fitar da shi cikinsa Jami' al-Ahkam al-Kur'an da ruwayar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, juzu'i na 16, shafi na 21-22.

[13] Tabataba'i daga Sheik Tusi.

[14] Wannan tawaga ta kumshi manya-manyan shuwagabannin kiristocin kamar haka: Abdul Masih, wanda ya kasance shugabansu, da kuma al-Ayhma, wanda ya kasance mai kula da al'amurran gudanarwa da ayyukan ibada, da kuma Abu Hatam ibn Alkama, wanda ya kasance bishof ne kana kuma kula da makarantunsu. Dubi Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki a sashin gabatarwar marubuci.

[15] Yin 'yar kure tsakanin vangare biyu kan Allah Ya saukar da azaba a kan vangaren da ba ya kan gaskiya. A takaice dai yin la'ananneniya tsakanin vangarori biyu don gano wani vangare ne ya ke kan gaskiya.

[16] Ashabul Kisa' (ma'abuta mayafi), suna ne da ake kiran mutanen da suka kasance tare da Manzon Allah (S.A.W) cikin mayafinsa inda daga baya aka saukar da Ayar Tsarkakewa a gare su. Su ne kuwa: Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (A.S), kamar yadda aka ambata a baya.

[17] Tafsirul Kashshaf na Zamakhshari yayin tafsirin Surar Ali Imrana aya ta 61,

haka nan kuma ya zo cikin Tafsirin Tha'alabi daga Mujahid da Kalbi.

[18] Tafsirul Kabir na Fakhrurrazi a kan Ayar Mubahala.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 next