Tarihin Mace A Al'adu



Babban abin da al’ummar musulmi take fuskanta daga yammacin duniya shi ne rashin adalci da suke yi wa musulunci da jahilci ko da gangan, ta yadda suke jingina abin da suke gani a kasashe da yake gudana game da yanayin zamantakewar mace, kamar a kauyukan Masar, ko Iraki, ko Maroko, ko Yankin saharar tsibirin larabawa, da wasunsu, inda kekashewar zuciya da rashin imani ya yi musu kanta, duk suna nuna matsalolin mace ta hanyar hangen wauta da kauyanci na ‘yan sahara wadanda suka ci baya kuma suke zaluntar mace. Sai suke nuna wa duniya cewa wannan shi ne ainihin musulunci da koyarwarsa kamar yadda ake gani.

Abin takaici na wannan rashin adalcin shi ne, sun san cewa musulunci shi ne ya kai musu wayewa da ci gaba a karnonin da suka gabata, amma ba zaka taba samun su suna masu godiya ga wannan ni’ima tasa ba, ko kuma su shelantawa duniya hakikanin gaskiya, kuma abin da yake tabbatar mana cewa da gangan ne suke wannan muzantawar shi ne, ba yadda zasu dauko ci bayan da suke da shi da kuma rashin wayewa da suke fama da shi a wasu yankunan su, ko kuma su dauko lalacewar al’adu da suke fama da shi, su danganta shi da Kirintanci.

Jahiltar musulunci yana daya daga cikin matsalolin da yake fuskanta a wannan lokaci da muke ciki hatta daga musulmin kansu, akwai jahiltar musulunci da wasu ke yi musamman ma a kasashen Turai, Amurka[26], da sauran nahiyoyin da ba na musulmi ba. Wadannan sun jahilci mafi karancin koyarwar musulunci, kuma suna ma yi masa wata mummunar fahimta karkatacciya da take siffanta shi da siffofin bata, ta’addanci, zubar da jini, ci baya, da tsattsuran ra’ayi[27].

A takaice zamu iya karanta wannan babbar matsala cikin jawabin da shugaban kasar Jamus Roman Hutsog ya yi a ranar 10/1/1995 a lokacin bikin girmama baturiyar nan masaniyar kasashe da al’adun musulmi a kasar Jamus Anamari Shamel, mai adalci cikin abubuwan da take rubutawa ta fada a lokacin bukin kyautar zaman lafiya da kungiyar marubutan kasar Jamus ta ba ta. Ya yi maganar ne yana mai mayar da martani ga masu sukan kyautar zaman lafiya da aka ba wa Shamel saboda kawai tana kariya ga tunane-tunanen musulunci, kuma tana mu’amala da shi bisa gaskiya da adalci, kuma tana kira zuwa fahimtarsa da sauya mummunar surar da kafafan watsa labaran Turawa ke yi ga musulunci da musulmi. ya ce:­

“Akwai wani al’amari da ke bayyane karara cikin alaka da mu’amalarmu da musulunci a wannan lokacin da muke ciki da ba zamu yi karya ga ra’ayin da ya watsu a Jamus ba idan muka ce: Abin da ke zuwa cikin tunanin mafi yawanmu a duk lokacin da aka ambaci musulunci shi ne, dokokin ukuba na rashin tausayi, ko rashin sassaucin addini, ko zaluntar mace, ko tsaurin ra’ayi irin na adawa, don haka wannan yanayi na tunani tsukakke ya wajaba mu sauya shi, mu tuna da ambaliyar nan ta hasken musulunci wadda tun kafin karnoni shida ko bakwai ta kiyaye wa kasashen yammaci wani sashe babba na tsofaffin abubuwan tarihi (Duba tarihin falsafar musulunci ko tarihin musulunci), babu shakka wannan nau’in tunanin na yamma mai tsauri ne kuma maras adalci”.

A yankin karshe na maganarsa shugaban na Jamus ya yi bayanin cewa, jahiltar da Turawa suka yi wa musulunci shi ne dalilin adawarsu da shi, don haka za mu same shi yana cewa:

“Ashe ba ta yiyuwa dalilin rashin fahimtarmu ga musulunci ya zama shi ne ginuwarsa a kan asasai masu zurfi na al’umma mai riko da addini alhali mu masu riko ne da wani tafarki da bai yarda da addini ba? Don haka ya tabbata yaya za mu yi mu’amala da wannan nazari mai matsala? Shin ya yi daidai mu siffanta musulmi masu tsoron Allah da siffofin masu tsattsauran ra’ayi ‘yan ta’adda don kawai mun kasa riskar yadda zafin izgili ga wani yake a zukatan mabiya wasu addinai, ko kuwa saboda mun zama ba za mu iya gani wannan ingantacciyar fahimtar ba”?

Daga nan sai shugaban na Jamus ya bayyana cewa: Shi bai san musulunci yadda ya kamata ba sai bayan da ya karanta littattafan wannan mustashrika mai adalci “Shamel” sai ya ce:

“Tsinkayata ga irin wannan abu muhimmi na tarihin musulunci da hakikaninsa a halin yanzu bai fara ba sai ta hanyar littattafan Anamari Shamel, akwai kyakkyawan zaton kuma cewa wasu irina ma sun fuskanci irin wannan gwaji, hakika muna bukatar mu sanya abin da ya shige mana duhu na fahimtar junanmu”.

Sannan sai shugaban na Jamus ya yi kira da a fahimci musulunci don shata wani matsayi game da shi koma bayan matsayin da ya ginu a kan jahiltarsa yana mai ce wa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next