Tarihin Mace A Al'adu



Mu sani al’ummu daban-daban ne kuma suna da al’adu mabanbanta ne, wasu gada ake yi, wasu kuma ana tasirantuwa da su ne ta hanyar zamantakewa a wani waje, ko kuma daga yanayin dab’iar wuri.

Bari mu ga mace a al’ummu daban-daban da ba su da littafi na doka da aka saukar daga sama, kamar dadaddiyar kasar Sin, da Indiya, da Tsohuwar Masar, da Iran tsohuwa, wadanda sun yi tarayya wajan rashin ba wa mace ‘yancinta kowane iri ne kuwa, ko da na nufi, da abin da take so, da na aiki, ko cin gashin kanta, ana tilasata mata ne su yi tarayya cikin duk wahala, da kebantuwa da aikin gida, da na namiji kan komai.

Na’am tana da dan samun ‘yanci na ta rayu cikin al’ummar da take kamar irin ta daji, domin a al’ummunsu ta kan yi gado da aure duk da ba ta da wani cikkakken ‘yanci, namiji ya kan yi aure ba iyaka a wajansu ya kuma kori wacce ya so, idan ya mutu ba ta isa ta yi wani aure ba, amma shi namiji yana da hakkin wannan, haka yake har a irinsu Iran kafin shigar Musulunci, kuma har ila yau a mafi yawancin wannan yankuna namiji yana iya taskace ta a gida ko duk inda ya so.

Wani lokaci zalunci ya taimaka wajan haifar da wasu tunani a tarihin wasu al’ummu, kamar ‘yan Addinin Mazdak da saboda zaluncin sarakuna, da kwace mata masu kyau daga hannun talakawa, sai suka yi tawaye suka haifar da wata fikira ta ban mamaki mai ganin cewa; Ai mace kamar sauran kaya ne babu batun ga matar wane ko ta wancan, duk wacce ka hadu da ita taka ce a wannan lokaci har ku rabu, kuma gobe kana iya kama wata, kamar dai kayan kasa a nazarin kominisanci, kamar yadda suka zo da fikirar juyin nan na cewa; kaya da dukiya da hakkin karatu na kowa ne ba na Sarki da ‘ya’yansa ba ne .

Duba ka ga Manbuzun (Untouchable) a Indiya wato dabakar Bakar fata da mace haramun ne ta kalle su don kawai kabilanci da mummunar wariyar launin fata da ta dasu a cikin jinin Ariyawa sama da shekara dubu hudu da suka gabata, domin kada mace farar fata ‘yar kabilar Ariyawa ta ji tana son Bakar fata, sai aka haramta wa mace kallon manbuzun aka kuma haramta mata hatta da taba duk abin da hannunsa ya taba, a sakamakon irin wannan mummunar wariya ce aka hana mace ‘yancinta, ta wani bangare kuma aka wulakanta mazaunan Indiya na asali wato Bakar fatar wajan da har yanzu akwai tasirin wannan kabilanci a jinin Ariyawa[4].

Haka ma Farisa a zamanin da, da tsarin dabakoki ya haifar wa dangin sarauta halaccin iya auren uwa da ‘ya da ‘yar’uwa a matsayin kishiyoyin juna domin kada jinin ya watsu a cikin wasunsu, kuma wannan tsarin ya rage kaifin zalunci kan dabakar mata saboda damar da ‘Ya’yan sarki mata suke da ita ta suna iya rike sarauta da tafiyar da al’amuran hukuma[5].

Mace A kasar Cana (kasar Sin)

A Tsohuwar Cana (kasar sin) auren mace kamar saye ne da mallakarta, kuma ba ta da gado ko ikon cin abinci tare da ita, kai har da ‘ya’yanta ba zai yiwu ba, Kuma maza da yawa suna iya tarayya a kan mace daya kamar yadda ake hada hannu wajan sayan mota ko doki, da jin dadi da ita, amma ‘ya’yanta na wanda ya fi saura karfi ne[6].

Mace A kasar Indiya

A Indiya mace na bin mijinta ne a samuwa, kuma ba ta da ikon yin aure bayan mutuwarsa, kai ana kona ta da ranta ne tare da gawar mijinta[7]. A Addinin Hindu idan mata suna haila to sun zama dauda haka ma duka abin da suka taba da tufafinsu kuma dole ne a nisance su, haka nan suna ganin cewa; ita wata halitta ce tsakanin mutum da dabbobi[8].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next