Tarihin Mace A Al'aduhfazah@yahoo.com Rabi’ul Awwl 1424 H.k Khurdad 1382 H.SH Mayu 2003. M Bayani Game Da Mace Saudayawa a kan yi tambaya menene hakikanin mace da matsayinta a al’umma, da tasirinta a rayuwar mutane, da hakkokinta, da hukunce-hukunce da suka shafe ta da asasinsu? kamar yadda a A kasashen Afrika Da Gabas Mai Nisa Idan muka duba rayuwar mace a al’ummu na wasu yankunan Australiya, da wasu yankunan Afrika, da Tsibiran Rasha, da na Tekun Pasifik, da Tsohuwar Amurka, rayuwar tasu tana daidai da rayuwar dabbobin ni’ima ce. An dauke su kamar tumakai ne da akan sayar a yanka, a wasu wurare ba ta ma kai ta su kima ba domin a yawacin wadannan yankuna namiji yana da ikon mallakarta kamar yadda ake mallakar dabbobi, kuma a amfana daga gare su kamar yadda ake amfana daga nonon wadannan dabbobi, a kuma sanya su yin noma da farauta da saurransu[2]. A wasu wurare suna ganin kamar an yi ta ne don namiji kawai samuwarta kafin aure da bayan aure tana bin ta maza ne sake ba kaidi, a wasu wurare ana sayar da su ne ba aura ba, ana ma iya bayar da rancensu, da aronsu, domin ta haihu ko tayi wata hidima, har ma ana iya kashe ta kuma babu kisasi ko a bar ta har mutuwa. Dukiyarta kuwa ta namiji ce haka ma duka wani abu da ta mallaka, haka ma komai na gida na wahala yana kanta kamar hidimar ‘ya’ya, da bukatun namiji, da sana’a, kuma dole ta jure ba yadda za ta yi, wani abin mamaki a wasu kabilu da mace ta haihu dole ta tashi don yin aikin gida a ranar[3]. Tsofaffin Addinai
|