Kurkuku Bincike Da Hukunci



·   Tanadar musu duk kayan lafiya da iska mai kyau da haske da kayan dumama daki da na sanyaya daki.

·   Tanadar musu kayan lafiya da tsaftace su.

·   Bandakin wanka da na ba haya mai tsafta.

·   Tufafi da shimfida da abinci da ruwan sha masu tsafta.

·   Wajan wasa na musamman da likitan nafs (ruhi da tunani) da na rashin lafiyar jiki da tanadin waje na musamman ga matan da suka haihu a furzin domin renon ‘ya’yansu.

·   Hana wasu su rika zaluntar wasu a furzin da hana yi wa dan furzin ukuba sau biyu a kan wani laifi da ya maimaita shi.

·   Hana azabtar da shi ko daure shi da sarka da mari da sauran nau’i na ukubobi.

·   Rubuta musu nau’i da dokokin Gidan Sarkar da suke ciki, tare da ba su damar shigar da kara ko neman wani abu da suke so, ko yin talpon zuwa ga iyalansu ko abokan arzikinsu da lauyansu da sauransu.

·   Ba su damar amfani da radiyo da talabijin da jarida da sauransu.

·   Samar musu da laburare a furzin domin nazari da bincike.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next