Kurkuku Bincike Da Hukunci



 

SAURAN CAJI

A kwai hanyoyi da dama da a kan dauka wajan cajin wanda ya ki biyan kudinsa na diyya ko hakkin mutane, wannan ya hada da wani caji da dauri da sauaransu. Masu laifin da a kan samu da cuta ta hauka a wasu kasashe saudayawa a kan kai su asibitoci domin binciken lafiyarsu, idan ba zai iya warkewa ba wasu kasashen sukan yi umarni da a sake shi, amma a wasu kasashe ba su da halin ko in kula game da wannan.

Kamar yadda yake laifuffuka iri-iri ne kuma suna da yawa kuma kowanne a kasashe da dama da akwai matakai da a kan dauka akansa, misali a wasu kasashen uban da ya zo wa 'yarsa ana zartar da cire wilaya da hakkin ubantaka daga gare shi ne, shugaban wani kampani idan ya ci hanci ana saukar da shi daga mukaminsa, ko kuma mai wani mukami idan ya karbi cin hanci ana haramta masa wani mukamin a kasa ne, amma maganarmu da yake game da Gidan Sarka ne shi ya sa ba zamu kawo su a nan ba.

 

DUNIYARMU A YAU

 

DAGA FURZIN ZUWA MATSAYI MAI GIRMA

Wani lokaci a kan samu wasu mutane sun shiga furzin saboda siyasa sai su fito su zama wasu manya sakamakon haka a duniya ko a kasashensu, kamar yadda wani lokaci masu laifi in sun shiga sai su fito sun kara kwasakwasai na kara wasu manyan laifuffukan. Duba Nkrumah da ya fito daga furzin na shekara daya kawai sai ga shi ya zama farkon Fira Ministan kasar Ghana a watan March 1957, tare da samun 'yancin kasar Gold Coast wato kasar Ghana a sunanta na da da yake nufin Gabar Zinare, amma sai ga gwamnatinsa ta halatta yin Gidan Sarka a 1958.

 

CI GABA A TSARIN GIDAN SARKA

Wata kasa daga kasashen Turai a kwanannan ne ta fara dawowa kusan samfurin furzin a musulunci kwanan nan, ta yadda tsarin Gidan Sarka ya zamana ta hanyar hana mai laifi fita daga gidansa ne sai ya zauna cikin iyalinsa, a tare da shi akwai wani inji kamar agogo da a kan sanya shi a hannu ko kafarsa da duk inda za shi abin yana iya nunawa ta kwamfitar jami'an tsaro cewa ya fita yawo, (kasuwa ko wani waje wato ya saba doka kenan) kuma a kan haka suna iya yi masa wani hukuncin.

Kamar yadda a kasar Amerika da wasu kasashen aka fara bude sana'o'i ga 'yan Gidan Kaso kamar saka da kafintanci da sana'anta takalama, koda yake wannan tsari ya dade a wasu kasashen sai dai ba su iya ganin kowa sai ma'aikata da kuma mai ziyara idan ya zo da dinki.

Haka nan aka bullo da tsarin gwaji a kasar Irish, idan lokacin sakin fursuna ya kusa da wata shida sai a mayar da su wajan da ake tsaro babu makami a hannun jami'ai, kuma a kan basu wasu 'yanci da ba kasafai fursuna ya cancance shi ba. Koda yake farkon shiga fursun suna kebe mai laifi shi kadai ne, sa'annan mataki na biyu a mayar da shi cikin sauran fursunoni, sannan matakin da muka fada a sama. A kwai Magana a game da nau'o'in furzin a duniya da ba zamu iya samun kawo shi a nan ba.

 

TSARE-TSARE DA MATAKAN MAJALISAR

 

DINKIN DUNIYA

A kwai tsare tsare da dama da kasashe suke da shi game da furzin kamar kasar Irish, koda yake ba zamu samu damar ci gaba da kawo irin wadannan bayanai ba amma zamu yi nuni da Majalisar Dinkin Duniya da sababbin tsare tsaren da aka tabbatar a taron Janiba.

A taron da aka yi na Majalisar Dinkin Duniya a Janiba a kasar Siwis a shekarar 1955. An kafa wasu dokoki da suka shafi furzina da hukunce hukuncen Gidan Sarka a cikin kusan doka 93. Anan zamu kawo maka wasu daga ciki ne kamar haka, musamman da yake sun dace da hankali:

·   Kula da ranar da fursunoni suka shiga furzin da laifinsu da sunansu da rashin karbar fursuna sai da wannan.

·   Rarraba fursunoni bisa la’akari da jinsinsu da shekarunsu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next