Kurkuku Bincike Da Hukunci



Saudayawa a kan hana ‘yan furzin haduwa da iyalansu da hana su ‘yancin walwalarsu da makamantan wannan, wannan kan iya haifar musu da cututtuka na lafiya da na ruhi sakamakon haka, har ma wasu suna haukacewa saboda hakan, al’amarin da yakan kai su ga Istimna’i (muguwar al’adan nan ta fitar da mani) da hannayensu ko kuma luwadi da yaduwar cututtuka kamar na fatar jiki da sauran miyagun cututtuka masu hadari. Kamar yadda wadanda ake tsarewa mudda mai tsayi kamar sama da shekara daya yakan iya kai matansu ko ‘ya’yansu da suke karkashin kulawarsu ga lalacewa da kuma zinace zinace.

7. Daduwar laifuffuka:

Mafi yawancin laifuffukan da ake tsare mutane domin aikata su ba su ragu ba har yanzu a duniya, sannan kuma kashi saba’in cikin dari na laifuffukan da ake tsare mutane a kansu a shari’ar Musulunci hukuncinsu ba tsarewa ba ne, misalin da zamu iya kawowa shi ne; Yawancin laifuffukan da suka yi yawa a duniya da a kan tsare mutane a kansu sun hada da sata, da sane, da fashi, da bashi, da rigimar aure, da fyade, da kisa, da tuhuma, da kusantar na jini da fasadin zina, da ta’addanci, da nuna rashin yarda ta hanyar jerin gwano, da zamba cikin aminci, da haijakin, da abubuwa da dama da wadansu imma laifi ne amma hukuncinsa ba dauri ba ne ko kuma abin da ba ma laifin ba ne kamar nuna ra’ayi ta hanyar jerin gwano na lumana.

Ta haka ne ‘yan Gidan Sarka suka yawaita a duniya bisa zalunci da take hakkinsu na walwala da shakatawa a matsayinsu na dan Adam, da kuma danne hakkinsu na kusantar iyalansu, da ganawa da ‘yan’uwansu na jini, da sauran al’ummar da suke rayuwa a cikinta, har ma yanzu ya zama akwai wani mummunan zaluncin da duniya ta dauka ci gaba ne wato hana magana tsakanin tsararre da danginsa sai ta bayan gilas da yana ganinsu suna ganinsa amma suna magana ta hanyar talpon ne, saboda haka ne ba abin da zai iya maganin yawaitar ‘yan furzin sai komawa ga Allah da la’akari da dokokinsa na asali kamar yadda Manzon Rahama (S.A.W) ya zo da su, da hikimar da take cikinsu, don haka masu kafa doka yana da kyau su nemi shawara daga masu tunani, marubuta, masu bincike game da Musulunci, kamar shi marubucin.

 

MENENE FURZIN

Akwai tambaya a kan cewa, shin furzin Haddi ne ko kuma Ta’aziri? (Ukubar da ba ta da wani haddi da aka iyakace aka kuma sanya shi a hannun HakimusShar’i) ko kuma wani abu ne da ya saba da wadannan abubuwa biyu? Kamar yadda ake bincike kan hikimar da ke cikin tsare mai laifi, kamar tsare mai sata a matakin sata ta uku, wanda wannan yana daga hikimar kare sharrinsa daga al’umma ne tunda ba zai shiriya da yanke ‘yan yatsun hannun dama guda hudu, da na kafar hagu ba. Al’amarin da yake nuna har yanzu dukiyar mutane ba ta kubuta daga sharrinsa ba, shi ya sa idan salihancinsa ya bayyana to a nan HakimusShar’i yana iya sakinsa. Haka nan tsare mutum idan ya kasance ta hanyar ta’aziri ne to wannan yana iya yiwuwa idan shugaba ya ga alamar na dama a tare da shi ya yafe masa ya sake shi, sabanin idan ya kasance bisa haddi ne. Kamar yadda ana iya tsare mutum a waje na musamman idan an san yana iya guduwa kafin a gama binciken tuhumar da ake yi masa, amma ya zama daidai gwargwadon lokacin da ya zama na lalura, haka nan kuma kada a wakilta mai gaba da mutum tsare shi domin yana iya kuntata masa sama da abin da shari’a ta yarda da shi, da sauran dokoki masu yawa da suke nuna menenen furzin da bincike ne masu tsayi da nan ba mahallinsu ba ne.

 

LAIFI DA MAI LAIFI

Ba ya halatta a ci mutuncin mai laifi koda kuwa kowane iri ne, ko kuma a nuna shi a talabijin ko a rika hira da shi a ciki domin wannan yana cikin keta alfarmarsa da Allah ya wajabta wa al’umma kiyaye ta, sai da wasu laifuffuka da hukunci ya zo da halarcin haka a kansu kamar mai kazafi kan mutane da sauransu, saboda haka abin da ake yi a wannan zamani yana daga abubuwan da aka haramta yin su game da mai laifi. Duba ka ga Hadisai da suka zo kan haramci mai tsanani da zunubi mai girma kan wanda ya bayyana asirin wani ko kuma ya wulakanta shi[9]. A cikin dokokin Jamhuriyyar Musulunci a Iran ya zo kamar haka: “Keta alfarmar da cin mutuncin kowane irin mutum ne da aka kama ko aka tsare ko aka rufe ko aka kora da hukuncin doka ta kowace hanya haramun ne kuma akwai sakamako mummuna mai yawa a kan haka[10]”. Wannan ya sanya hatta da dan sanda ba shi da ikon taba mai laifi sai dai ya kai ka ga kotu, domin ya sake ya taba shi zai shigar da shi kara kotu, haka nan mutane duk wanda ya yi maka wani abu kana iya gurfanar da shi kotu a bi maka hakkinka.

Akwai laifuffukan da shari’a ta zo da hukuncin tsare mai yin su, amma bayaninsu cikakke yana cikin littafan shari’a domin wasu ana tsare su idan sun ki aikata wani abin kamar diyya ko tara ko fansa kamar haka:

1.   Mace mai ridda daurin rai da rai har sai ta tuba.

2.   Mai sane da mai yankan aljihu da mai tona kabari.

3.   Wanda ya aske wa wata mata kanta yana mai yi mata tilas.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next